Ciwon tundurmi da na gwaiwa
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Ciwon tundurmi da na gwaiwa

Me ke haddasawa wasu mutane ciwon gwaiwa? Mene ne illarsa ga lafiyar mai dauke da ita? Ana gadonta ko ana daukar ta ne? Ana cireta kwata-kwata?

Amsa: A Hausance duk wata matsala da ta sa kumburi a jakar da ta lullube maraina ko kwalatai akan kirata gwaiwa, a wasu lokuta ma har da kumburin su marainan akan hada a kirasu haka. Don haka ne ma wasu kan yi kuskuren alakanta   kaba (zazzagowar hanji cikin maraina), wanda shi ma zai iya sa a ga kamar kumburi a jakar marainan, da ciwon gwaiwa.

Amma dai a kimiyyance abin da ke sa gwaiwa kusan an kusa magance ciwon a wannan kasa. Wannan ciwo kuwa shi ne ciwon tundurmi, wanda kan sa kumburin kafafu da na jakar maraina. A ’yan shekarun baya, mutane da dama sun yi fama da irin wannan matsala, amma idan aka yi la’akari da hobbasar hukumomin lafiya na kasar nan tare da hadin gwiwar na kasashen waje, wajen ganin an kawar da wannan ciwo na tundurmi a kasar nan, (kamar yadda suka yaki ciwon kurkunu), a yanzu da wuya a ga sabbin kamu, idan an ga masu irin wannan kumburi sai dai tsoffin kamu. 

Shi ciwon tundurmi sauro ne ke yada shi bayan ya ciji mai ciwon ya kwaso kwayoyin cutar, sai ya sa wa wanda bai da shiu. Sauron amma ba dole sai irin mai sa ciwon maleriya ba, kowane irin nau’i zai iya yada kwayar cutar, mai kama da ‘yar karamar tsutsa. Ita wannan kwayar cuta, wadda ake kira Wuchereria, ita ke shiga wasu kananan magudanan jini karkashin fatar kafa da wadda ta lullube maraina ta kawo tundurmi da ciwon gwaiwa. 

Amma da yake ciwon ba wasu alamu yake kawowa na zafin jiki da zazzabi da laulayi ba, in ban da shi kansa kumburin, wanda sai bayan shekaru da shigar ciwon ma akan gan shi, wasu ba su ma san suna da shi ba, ballantana su nemi magani. Sai fa kumburin ya faru ake ganowa. 

To amma idan aka ga kumburin, kusan ciwon ya riga ya yi illa, domin ko an nemi magani, kwayoyin cutar kawai maganin kan kashe, amma wannan nakasa ta kumburi zai wahala ta bace. Shi ya sa aka yi ta ba da magungunan kariya a yankunan da matsalar ta yi kamari a shekarun baya, aikin da kungiyar Carter Center ta Amurka ta jagoranta. 

Har yanzu a kasar nan akwai wadanda ciwon ya nakasa, wadanda ko sun nemi magani ko basu nema ba, sun dai yi amfani da wannan dama sun maida kansu musakai suka koma yin barace-barace.

 

Ina yawan jin zafin mara. Domin sai ta kulle na kasa sakat. Dama ba mata kadai ba ne ke ciwon mara?

 

Daga Murtala, kwalli

Amsa: E, haka ne kullewar mara a mata ya fi yawa ba a maza ba, domin idan aka yi la’akari da halittar matan da ta mazan, akwai bambance-bambance na mahaifa da gajartar mafitsara da sauransu. A maza idan aka samu hakan an fi dangantashi da matsalar hanyoyin fitsari, wato tantanin tara fitsari ko igiyoyin da suka shigo cikinta daga koda. Abubuwan kuwa da suka fi sa kullewar marar a mazan kusan an sha fadarsu a nan, kuma ba su wuce tsakuwa a mafitsarar ko kwayoyin cuta ba. Ke nan mai samun irin wannan akai-akai sai ya nemi asibiti sosai an bincika an ga wanne ne daga cikin wadannan.

 

Shin da gaske ne gauta na iya sa matsalar basir?

 

Daga A.B, Kaduna

Amsa: A’a a likitance duk wani abinci na kayan ganye da ‘ya’yan itace ko busasshe ne ba zai iya sa basur ba, sai dai abinci wadanda suke masu tauri, ko masu sa taurin bayan-gida. Tun da ka ga gauta ma ai daga albarkatun ‘ya’yan itatuwa ne, wato na data.

 

Ni kuma idan na yi bayan gida sai na kai kusan kwanaki hudu ko biyar kafin na sake tsugunawa. Ko hakan matsala ce?

 

Daga Rabiu, Kano

Amsa: E, kuma a’a, musamman ma idan ba ka samun taurin bayan gida, domin akwai bambancin jiki - wani sai ya tsuguna a kullum, wani sai bayan kwana biyu ko uku, wani sai a rana ta hudu. To kusan idan hudun ne ke nan ba matsala, amma a ce an je kwanaki biyar, lallai sai ka kara yawan ‘ya’yan itatuwa da ganyaye a cimakarka.

Haka nan sai na ji girar idona na motsi. Ko hakan na nuni da wata matsala ne?

 

Daga Yusuf, Funtua 

Amsa: A’a ba wata matsala, sai dai idan kana jin zafi ko zogi idan abin na yi. Domin ai a jikinmu kusan kowane motsi muke akwai tsoka mai daukar alhakin aikin motsa wurin. Wato dai tsoka ce ta karkashin gira take motsi haka kawai, kamar yadda a wasu lokuta za ka ji naman cinyarka na motsawa, musamman idan kai mai yawan motsa jiki ne.

 

Ni kuma saurin fushi ne da ni, amma sai abokaina su ce wai saboda yawan cin yaji da nake ne. Mene ne gaskiyar wannan a kimiyyance? Wace shawara za a iya ba ni?

 

Daga Haidar danKurma

 

Amsa: A’a ba dai yaji ba, sai dai ko kurumta, tunda ana ce maka dankurma. An sani cewa a halaiyar zamantakewa masu wannan suna na da saurin fushi. Wato a iya cewa ke nan dai a yanayin halayya ne ba a cimaka ba. Ke nan saurin fushi dabi’a ce, ko hali, wanda kan sa wasu sinadarai su taru a kwakwalwa fiye da kima. Kuma idan mutum ya sa kansa zai iya dainawa tunda shi saurin fushin ba shi da wani amfani sai dai ma akasi. Babbar hanyar da mutane masu saurin fushi ya kamata su bi ita ce ta saurin jan dogon numfashi yayin da aka bata musu rai, sa’annan sai ya yi tunani akan abin - shin abin ya kai a ma a masa fushi ko dai kawai mai wucewa ne na dan lokaci.

Daga Haruna Muhammad, Katsina
Amsa: A Hausance duk wata matsala da ta sa kumburi a jakar da ta lullube maraina ko kwalatai akan kirata gwaiwa, a wasu lokuta ma har da kumburin su marainan akan hada a kirasu haka. Don haka ne ma wasu kan yi kuskuren alakanta   kaba (zazzagowar hanji cikin maraina), wanda shi ma zai iya sa a ga kamar kumburi a jakar marainan, da ciwon gwaiwa.Amma dai a kimiyyance abin da ke sa gwaiwa kusan an kusa magance ciwon a wannan kasa. Wannan ciwo kuwa shi ne ciwon tundurmi, wanda kan sa kumburin kafafu da na jakar maraina. A ’yan shekarun baya, mutane da dama sun yi fama da irin wannan matsala, amma idan aka yi la’akari da hobbasar hukumomin lafiya na kasar nan tare da hadin gwiwar na kasashen waje, wajen ganin an kawar da wannan ciwo na tundurmi a kasar nan, (kamar yadda suka yaki ciwon kurkunu), a yanzu da wuya a ga sabbin kamu, idan an ga masu irin wannan kumburi sai dai tsoffin kamu. Shi ciwon tundurmi sauro ne ke yada shi bayan ya ciji mai ciwon ya kwaso kwayoyin cutar, sai ya sa wa wanda bai da shiu. Sauron amma ba dole sai irin mai sa ciwon maleriya ba, kowane irin nau’i zai iya yada kwayar cutar, mai kama da ‘yar karamar tsutsa. Ita wannan kwayar cuta, wadda ake kira Wuchereria, ita ke shiga wasu kananan magudanan jini karkashin fatar kafa da wadda ta lullube maraina ta kawo tundurmi da ciwon gwaiwa. Amma da yake ciwon ba wasu alamu yake kawowa na zafin jiki da zazzabi da laulayi ba, in ban da shi kansa kumburin, wanda sai bayan shekaru da shigar ciwon ma akan gan shi, wasu ba su ma san suna da shi ba, ballantana su nemi magani. Sai fa kumburin ya faru ake ganowa. To amma idan aka ga kumburin, kusan ciwon ya riga ya yi illa, domin ko an nemi magani, kwayoyin cutar kawai maganin kan kashe, amma wannan nakasa ta kumburi zai wahala ta bace. Shi ya sa aka yi ta ba da magungunan kariya a yankunan da matsalar ta yi kamari a shekarun baya, aikin da kungiyar Carter Center ta Amurka ta jagoranta. Har yanzu a kasar nan akwai wadanda ciwon ya nakasa, wadanda ko sun nemi magani ko basu nema ba, sun dai yi amfani da wannan dama sun maida kansu musakai suka koma yin barace-barace.
Ina yawan jin zafin mara. Domin sai ta kulle na kasa sakat. Dama ba mata kadai ba ne ke ciwon mara?
Daga Murtala, kwalliAmsa: E, haka ne kullewar mara a mata ya fi yawa ba a maza ba, domin idan aka yi la’akari da halittar matan da ta mazan, akwai bambance-bambance na mahaifa da gajartar mafitsara da sauransu. A maza idan aka samu hakan an fi dangantashi da matsalar hanyoyin fitsari, wato tantanin tara fitsari ko igiyoyin da suka shigo cikinta daga koda. Abubuwan kuwa da suka fi sa kullewar marar a mazan kusan an sha fadarsu a nan, kuma ba su wuce tsakuwa a mafitsarar ko kwayoyin cuta ba. Ke nan mai samun irin wannan akai-akai sai ya nemi asibiti sosai an bincika an ga wanne ne daga cikin wadannan.
Shin da gaske ne gauta na iya sa matsalar basir?
Daga A.B, KadunaAmsa: A’a a likitance duk wani abinci na kayan ganye da ‘ya’yan itace ko busasshe ne ba zai iya sa basur ba, sai dai abinci wadanda suke masu tauri, ko masu sa taurin bayan-gida. Tun da ka ga gauta ma ai daga albarkatun ‘ya’yan itatuwa ne, wato na data.
Ni kuma idan na yi bayan gida sai na kai kusan kwanaki hudu ko biyar kafin na sake tsugunawa. Ko hakan matsala ce?
Daga Rabiu, KanoAmsa: E, kuma a’a, musamman ma idan ba ka samun taurin bayan gida, domin akwai bambancin jiki - wani sai ya tsuguna a kullum, wani sai bayan kwana biyu ko uku, wani sai a rana ta hudu. To kusan idan hudun ne ke nan ba matsala, amma a ce an je kwanaki biyar, lallai sai ka kara yawan ‘ya’yan itatuwa da ganyaye a cimakarka.Haka nan sai na ji girar idona na motsi. Ko hakan na nuni da wata matsala ne?
Daga Yusuf, Funtua Amsa: A’a ba wata matsala, sai dai idan kana jin zafi ko zogi idan abin na yi. Domin ai a jikinmu kusan kowane motsi muke akwai tsoka mai daukar alhakin aikin motsa wurin. Wato dai tsoka ce ta karkashin gira take motsi haka kawai, kamar yadda a wasu lokuta za ka ji naman cinyarka na motsawa, musamman idan kai mai yawan motsa jiki ne.
Ni kuma saurin fushi ne da ni, amma sai abokaina su ce wai saboda yawan cin yaji da nake ne. Mene ne gaskiyar wannan a kimiyyance? Wace shawara za a iya ba ni?
Daga Haidar danKurmaAmsa: A’a ba dai yaji ba, sai dai ko kurumta, tunda ana ce maka dankurma. An sani cewa a halaiyar zamantakewa masu wannan suna na da saurin fushi. Wato a iya cewa ke nan dai a yanayin halayya ne ba a cimaka ba. Ke nan saurin fushi dabi’a ce, ko hali, wanda kan sa wasu sinadarai su taru a kwakwalwa fiye da kima. Kuma idan mutum ya sa kansa zai iya dainawa tunda shi saurin fushin ba shi da wani amfani sai dai ma akasi. Babbar hanyar da mutane masu saurin fushi ya kamata su bi ita ce ta saurin jan dogon numfashi yayin da aka bata musu rai, sa’annan sai ya yi tunani akan abin - shin abin ya kai a ma a masa fushi ko dai kawai mai wucewa ne na dan lokaci.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited