Amsoshin Tambayoyi
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Amsoshin Tambayoyi

Qwaya Ankwa ceIna da matsalar kaba, na je asibiti an duba ni an ba ni kwanakin aiki zuwa wata huxu. To ga shi kuma kafin lokacin za a kirani aikin soja. Ko akwai magungunan da zan iya sha kafin lokacin?

Daga T. M. M

Amsa: Wannan tambaya taka tana da amfani, kuma tana da sarkakiya, amma na so a ce likitocin da suka ba ka ranar aikin sun san da wannan batu, domin suma su ba ka shawarar da za ta fi dacewa. Ko da ka same su dai xayan biyu za a yi; ko dai ka jinkirta aikin soja ko kuma ka jinkirta aikin kaba. Domin ita kaba ba a ba ta magunguna, sai tiyata.

To inda sarkakiyar take shi ne, idan ka ce za ka aikin atisaye na xaukar soja da kabar kafin a yi aikin, jidalin atisayen zai iya illata kabar, ko dai ta kara girma, ko kuma ta murxe maka ’ya’yan hanji, a zo ana sai an yi aikin gaggawa na Emergency. Ka ji xaya. Idan kuma ka ce a gaggauta yi maka aikin kabar kafin ka tafi atisayen, shi ma dai akwai yiwuwar jidalin atisayen ya dawo da matsalar, domin kuwa duk wanda aka wa aikin kaba ana so ya guji aikin wahala ko na karfi ko na xaukar nauyi na tsawon watanni, dangane da inda kabar take.

To ka ji abin da ya sa aka ce wannan magana ta fi karfin a rubuce, sai ka je wurin likitan naka gaba-da-gaba kun tattauna, kun yanke shawara mece ce mafita a gareka, a ga abin da zai fi maka wanda ba zai taba lafiyarka ba, kuma wanda watakila ba zai shafi wannan buri naka na aikin soja ba.

Ina fama da wata matsala a gefen cikina, sa’annan idan zan yi fitsari ina jin zafi bayan na gama. Na je asibiti an ba ni magunguna amma ba sauki. Ko mece ce shawara?

Daga Mustapha Idris

Amsa: Eh, wannan bayani yana kama da na wanda kwayoyin cuta suka shigar wa mafitsara. Tabbas idan aka ba da maganin kashe kwayoyin cutar sukan mutu, mutum ya ji daidai. Matsalar takan zo ne idan magungunan da aka ba ka ba su ya kamata a ba ka ba, musamman idan ba a yi gwajin fitsarin an ga irin kwayoyin cuta da magungunan da suka dace a bayar ba, ko kuma idan an ba da magungunan ba a sha su yadda aka tsara a sha su ba.

Da gaske ne goro yakan iya yi wa zuciya illa kamar yadda sigari kan yi?

Daga Abubakar Usman, Gombe

Amsa: Ai ba xaya suke ba Malam Abu, ita sigari ba a kwatanta da komai sai dai watakila tabar wiwi ko ma ruwan barasa ko sauran kayan maye. Domin ita sigari ana ganin sinadaran guba a cikinta sun fi a kirga. Shi goro abin da za a iya kwatanta shi da shi shi ne ganyen shayi na Coffee, tunda sinadaransu iri xaya ne - da goro da coffee duk sinadarin Caffeine ne a cikinsu. Shi wannan sinadari ba ya sa ciwon daji kamar yadda sauran sindaran waxancan kayan maye sukan sa, wato Nicotine da sauran gubar da ke cikinsu. Abin da yakan sa shi ne ciwon naci, wato Addiction, idan ba a sha ba ba a jin daxi. Don haka ne a kan ce mutum ya xan rika yi wa kansa faxa a kansu tun kafin su fi karfinsa.

Ni ina tu’ammali da kwaya, na tsawon shekaru uku. Na yi kokari na daina amma idan na bari sai na ji ba na jin daxin jikina. Amma da na sha shike nan. Ko mece ce shawara yadda zan magance wannan matsala?

Daga A.A, Abuja

Amsa: Yauwa to ka ji wanda shi abin ya ma fi karfinsa ke nan. Wato kai a taka matsalar abin ya yi kamarin da kwakwalwarka ba ta so ta rabu da kwayar ke nan, shi ya sa da ka bari take dugunzuma ta rika sakin sinadarai masu hana ka sakat. To a gaskiya kamar yadda muka riga muka sha faxa ne, idan hakan ta faru, dole sai dai asibiti, asibiti kuma babba, bangaren likitocin kwakwalwa da tunanin xan Adam, kuma dole ka shirya kwanciya idan kana so a ci nasara, domin ko sun gan ka sun rubuta maka magani a banza, in dai za ku yi ido biyu da kwayar a wurin harkokinka na yau da kullum.  Domin kwaya ankwa ce, sai ka yi da gaske za ka iya kwance ta.

Wata ’yar uwata ce kimanin shekara ke nan take da matsala. Wani ciwo ne da ita wanda idan zai tashi sai idonta ya yi ja, ta kumbura ta rika ihu tana faxuwa kasa, tana jijjiga, baki na kumfa. Ko me ke damunta? Mece ce shawara?

Daga Hajiya A.

Amsa: To, wannan kam yana kama da wani ciwo a kwakwalwa. To amma da yake a yankin Arewa muna la’akari da addini da al’ada wajen yanke shawara, za a iya ba ki shawara biyu. Ciwo a kwakwalwa yana nufin a likitance akwai wani abu a kwakwalwa, tunda akwai cutuka a likitance masu sa haka, kamar na karancin wasu sinadarai a kwakwalwa, wanda akan kira da tabin hankali, ko kuma kwayoyin cuta da ba su cika shiga kwakwalwa ba, amma suka samu suka shiga, a mutane waxanda garkuwar jikinsu ta yi rauni, kamar masu ciwon kanjamau ko masu karancin abinci a jikinsu. Amma saboda wasu dalilai na addini, da al’ada, matsalar kuma za ta iya zama wani abu daban. Misali a nan shi ne a zamanin da aka yi wani ciwo wai sunbuka a wasu makarantun ’yan mata na kwana kawai, ba na maza ba, wasu malamai sun ba da fatawarsu, haka ma wasu likitoci sun ba da ta su fatawar, inda suka ce ita wannan rawar sunbukar, wato Chorea, akwai cutuka a likitance ma masu sa haka.

Don haka ke nan kuna da zabi biyu kuma dole ne a bi su duka biyun kafin a samu mafita. Ko dai ku fara zuwa wurin malamai masu rukiyya, su yi, idan sun tabbatar ba matsalar da ake hasashe bace, a kai ta asibiti a mata gwaje-gwaje da aune-aune don su gano matsalar, ko kuma a fara da asibitin kafin a je rukiyyar, duk dai wanda aka fara zaba.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited