LAFIYAR MATA DA YARA: Amsoshin Tambayoyi 1
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

LAFIYAR MATA DA YARA: Amsoshin Tambayoyi 1

Yarona ne tunda na haifeshi sai ya rika yawan shassheka ko ajiyar zuciya, ko da bai yi kuka ba, kuma ko barci yake. Ko akwai matsala ne?
Daga Maman Sudais, Katsina
Amsa: Eh, yawan ajiyar zuciya haka kawai ba tare da an yi kuka ba, zai iya nuni da matsalar hanyoyin numfashi ko ma na zuciyar baki daya, musamman ganin kin ce ga shi yaro na girma amma abu ba ya sauki.

Ni kuma ina son shawara ne. Ina da juna biyu watansa biyu kuma ina so na yi tafiya daga Katsina zuwa Bauchi. Ko hakan ba wata matsala?
Daga J.A
Amsa: A’a wannan tafiya tana da tsayi, domin akalla sai an yi awa shida ko sama da haka. Watakila kuma akwai rashin kyan hanya. Idan da son samu ne a jinkirta tafiyar ya fi, kamar idan ciki ya haura wata hudu zuwa biyar, za a iya zuwa, tunda ana ganin daga watanni hudu zuwa biyar hadarin zubewarsa ragagge ne. Shi wannan cikin dan wata biyu daga Katsina ai Zariya ko Kano kawai za a iya baki shawara ki je, shi ma sai da larura, tun da zuwa wadannan garuruwa ba zai wuce awa biyu ba.

Ina shan kwayoyin tsara iyali. Sai kuma na ji wasu suna cewa yana da matsala. Mece ce gaskiyar haka?
Daga Aisha, Zariya
Amsa: In dai likita ko ma’aikaciyar jiyya ce ta rubuta miki ba matsala. Amma idan da kanki kika je kika sayo, to akwai matsala, domin ba kowa ake ba wadannan kwayoyi ba (har ma da alluran) sai an dan yi aune-aune an tantance ko kina da wasu cutuka, kamar na hawan jini ko kiba, ko ciwon damuwa, ko ma wani ciwo na daban, sa’annan idan ta kama ma a yi gwaje-gwaje. Don haka ke nan ba da ka ake shansu ba - akwai wadanda bai kamata su sha ba.

A kimiyyance ko tagwaye na iya fidda kofi?
Daga Nasiru Kainuwa Hadejia
Amsa: Eh, kuma a’a. A kimiyyance an san akwai mutane masu baiwa iri-iri, da kan iya yin abubuwan al’ajabi wadanda ba kowa ke iya yi ba. Amma dai ba a dangantashi da ’yan biyu ko ma wani rukuni na mutane ba. A al’adance ne, ko addinance watakila akan danganta abin da wasu rukunin mutane.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited