Amsoshin Tambayoyi Daban-Daban 2
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Amsoshin Tambayoyi Daban-Daban 2

Ko aske gashin cikin hanci da kunne yana da wata fa’ida a likitance?
Daga Aminu Yakubu
Amsa: Wannan tambaya taka tana da muhimmanci sosai, domin akwai mutane da dama da ba su san amfanin gashin cikin hanci da na kunne ba. Gashin cikin hanci da na kunne suna daga cikin sassan jiki masu taimakawa wajen yakar kwayoyin cuta. Hikimarsu ita ce duk kwayar cutar da za ta shiga hancin ko kunnen su riketa kada ta shige, kai kuma idan ka tashi wanka sai ka sa hannu ka dan wankosu waje, ka ga an hana wasu kwayoyin cuta shiga jiki ke nan.
Yawan irin wannan gashi yakan bambanta daga wani zuwa wani. A wasu dan kadan ne, sai an kura ida sosai za a gani, a wasu kuma har lekowa waje suke. A wasu kuma akwai tsaka-tsaki. To masu shi da yawa din, wadanda yakan yi yawa har ya leko waje ba kyan gani, sune ake so su dan rika rageshi, ba askeshi tatas ba.
Sa’annan har ila yau, a can cikin hancin da kunnen, da ma hanyoyin numfashi akwai wasu nau’i na kananan gashi wadanda ido ba ya gani masu tare kwayoyin cuta, idan an yi tari ko atishawa a feso su waje.

Ni yau shekaru bakwai ke nan ba na ji sanadiyyar wani ciwon kafa. Na shiga asibitoci da yawa amma ban samu mafita ba. Shi ne na ke neman shawara.
Daga Binyamin, Ningi
Amsa: In dai a cikin asibitocin da ka je ba ka samu ka je na kunne ba, to da sauran yawo, sai dai fa idan baka son mafita. Tunda ban ji ka ambaci asibitin kunne ba. A sanina a nan garinku ba asibitin kunne. Hasali ma babban asibitin kunne na kasa a Kaduna yake, don haka zama bai same ka ba. Watakila ya kamata a jaddada wani batu da mutanenmu suke yawan mantawa. Ya kamata da kai da sauran masu karatu mu san cewa in dai da iko, ita lafiya, kamar ilmi da arziki, duk inda ta kama a je a nemo su, to fa wajibi ne a je, komai nisa, musamman idan babu a kusa.

Ina fama da ciwon ido har ta kai wani baki ya fara zagaye mini farin idon. Ko wannan matsala ce?
Daga Mubarak A.
Amsa: Eh, kwarai kuwa matsala ce, tunda ka ce akwai ciwo, kuma yana sauyawa daga yadda aka san lafiyayyen ido zuwa wani abu daban. Sai ka je an binciki idon kafin a iya gane ko mene ne.

Ina yawan yin shake ta hanci. Ko hakan na da wani amfani ga jikina?
Daga Abubakar S. Sokoto
Amsa: Shaken me? Hodar iblis ko me? A addinance da likitance banda shaken ruwa da wasu nau’ukan magani wadanda akan rubuta a asibiti, ba wani shake da aka sani. Duk wani abu ba wadannan ba, wanda mutum ya saya ya je ya shaka, duk abin da ya same shi shi ya jiwo.

Wai yawan karatu a zuci yana kawo ciwon zuciya?
Daga R.B.M., Kano
Amsa: Ka dai san ai abinda ake nufi da karatun zuci ko? Wato in an ce a zuci ba a zuciya abin yake ba, a’a a wurin tunani abin yake, wato kwakwalwa. An yi bayanin cewa kwakwalwarmu za ta iya daukar bayanai fiye da na na’urar kwamfuta. Bayanai da ke cikin kan wasu manyan malamai da wasu farfesoshi ma zai iya fin na na’urar kwamfuta. Sai dai karfin kwakwalwar wani bai kai ta wani ba, domin akwai wadanda idan kwakwalwarsa ta dauki bayanai da yawa za ta iya rikicewa, su dan samu tabin hankali.

Ni ba na wani ciwon ciki kawai rannan sai na ga wasu kananan macizan ciki a bayan gida. Me ke kawo su?
Daga Mustapha, Kano
Amsa: Daga cin nama ne. Ai mun sha bayani a nan, cewa dukkanmu masu cin nama za mu iya samun macizan ciki akai-akai, saboda dabbobinmu suna kiwon gargajiya, suna cin duk abin da suka samu a gida da titi. Wato daga dabbobinmu ne. A kasashen da aka ci gaba sosai, inda dabbobinsu ke kiwon zamani, wadanda cimakarsu sai an zabo, abin da sauki.
Mun ce ko mutum na da alamu, ko ba shi da su, duk shekara mutum ya kamata ya sha maganinsu. Yara kuma duk bayan watanni shida ya kamata su rika shan magungunan macizan cikin, kuma ba sai an rubuta maka su ba, kai tsaye su za a iya sayensu.

Na ji ka dan tabo bayanin ciwon Asma. Shin ana gadonta ne ko yaya?
Daga Maharazu Muhammad
Amsa: Eh, kwarai kuwa ana iya gadon ciwon Asma.

Ni idan ina dariya har hawaye kan zubo min. Ko matsala ce?
Daga Muhammad A.
Amsa: A’a wannan ba matsalar lafiya ba ce, akwai mutane masu samun haka, idan suna dariya har kwalla da hawaye kan iya fitowa.

Ni ina da kibar gado, shekaruna ba su wuce 22 ba amma idan ka ganni ka ce dan 60 ne. Don Allah a ba ni shawara yadda zan rageta.
Daga Bello A.
Amsa: Ai an sha fadar hanyoyin ragewar a nan. Sai dai bin hanyoyin ne ke da matukar wahala. Amma dai muhimmi daga ciki wanda za a iya cewa ya fi sauran aiki shi ne rage cimaka. Misali akwai wani yaro da muna tasowa a kuruciya mai kibar gado. An yi an yi ya ragu, an kasa, amma da aka kai shi makarantar gaba da firamare ta kwana, cikin watanni uku ya zabge, saboda karancin abinci da yawan zirga-zirga da wasanni. Har yanzu bai sake kiba ba. To kaima idan da za ka daure ka rage yawan cimakarka (idan an zubo maka abinci ka ce a rage kashi daya cikin uku), ka kuma rika yawan wasanni, cikin watanni kadan za ka ga canji.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited