LAFIYAR MATA DA YARA: Amsoshin Tambayoyi 02
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

LAFIYAR MATA DA YARA: Amsoshin Tambayoyi 02

Na samu bari kusan wata hudu da suka wuce, ko zan iya samun wani juna biyun cikin dan lokaci?
Daga Khadija S
Amsa: Wannan ita ce tambaya da mata da dama kan yi  wa likitoci bayan sun yi bari; wato wata nawa ya kamata a jira kafin a sake daukar wani cikin. Sababbin bayanai na binciken likitocin mata sun tabbatar da cewa an fi so idan mace ta yi bari to da al’ada ta daidaita, ba sauran jiran wasu watanni har ma wata hudu. Wasu ma kafin al’adarsu ta farko ta dawo sun riga sun samu wani juna biyun. Hakan shi ya fi, tun da binciken ya nuna cewa cikin da aka sake dauka tsakanin watanni 6 bayan bari zai wahala ya sake barewa. In kuma har ya sake zubewa to fa matsalar babba ce sai an kai ga bincike-bincike da aune-aune don gano matsalar.
Ka yi bayani cewa magungunan tsarin iyali sai an je asibiti. To ga shi ni an yi mani allurar shekaru biyar amma ba a asibiti ba. Ko zan iya samun matsala?
Daga Maman Sudais, Katsina
Amsa: kwarai da gaske kuwa, za ki iya samun matsala. Duk da dai baki fadi inda kika je aka yi maki ba. Ko kawai mai gidanki ne ya sawo ya maki ita da ka? Ko likita ce ko mai aikin jinya ko ungozoma bai kamata su yi maki allurar a gida ba, sai dai fa idan dama kin riga kin je asibitin aka ce za a zo gida a yi maki.
Yarona ne ke da wata ’yar huda a wuyansa tun da aka haife shi, ga shi yanzu ya kai shekaru 10. Ba ta masa komai sai dai yanzu na ga wani ruwa mai yauki na fitowa. Ko akwai matsala?
Daga A.M.
Amsa: E akan iya haifar yara da wata huda a wuyansu, ko ma kumburi mai kama da makoko, wadda kan faru sakamakon rashin rufewar fatar wuyan a wasu jariran tun suna ciki. A lokacin da kasusuwan wuya da tsoka da jijiyoyi ke hadewa su zama wuya, akan iya samun wata tangarda a wasu yaran wurin ya ki rufewa gaba daya, a zo a ga wata ’yar kafa ko huda, ko kumburi bayan an haifi jariri.
Idan a asibiti aka haifi jariri, ma’aikatan karbar haihuwa suka lura da irin wannan matsala, sukan kira likitocin fida su duba, idan ya dace a yi aiki a yi. Idan ma ba a yi aikin ba, a mafi yawan lokuta jaririn ba ya samun matsala, amma a wasu lokutan ana iya samun kwayoyin cuta su shiga ramin, ruwan miki ya fara fitowa. Idan aka samu haka, to akwai matsala kuma sai an kai likitocin tiyatar sun gani su ba da shawara ko sai an yi ’yar tiyatar rufe ta.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited