Shin ko kudin cizo na haddasa cututtuka?
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Shin ko kudin cizo na haddasa cututtuka?

Wai shin idan  kudin cizo ya ciji mutum yana sa wata cuta ne?
Amsa: Kudin cizo, wato wani dan karamin kwaro da a turance ake ce masa bed-bug, kwaro ne da kan iya addabar lafiyar dan Adam. Duk da yake dai a nan irin kasashenmu ba a ba da tabbacin wani ciwo guda daya da za a iya alakanta shi da wannan kwaro ba, ana ganin kwaron yana iya shan jini idan ya shiga ya buya ya yi cizo a karkashin fata. Haka nan shigarsa karkashin fatar yana iya jawo kaikayi da soshe-soshe, a kasa samun barci isasshe lokacin kwanciya, da yake cikin dare yake cizon.
Ana iya samun wadannan kwarin a kasashe da dama a duniya, tun daga kasashen nahiyar Amurka da nahiyoyin Turai da Asiya. Yawanci mutane ke yada su daga wannan wuri zuwa wancan a cikin jakunkuna da kayansu. Don haka ba abin mamaki ba ne a same su a gadon manya-manyan otal-otal da na fitatttun wuraren shakatawa, kuma a iya kwasarsu a kai gida ba a sani ba. Abin da ya sa ake iya daukarsu da yada su shi ne cewa sun iya buya, domin da wuya a gansu da rana, don sukan iya shigewa cikin yadin katifa ko kalmasar zanin gado, ta yadda sai duhu ya yi kafin su lallaba su fito, su fara cizo suna shan jini. Wannan cizo zai iya sa wurin ya fara kaikayi ya canza kala, sai dai bai kai cizon kuma (wasu nau’ukan kwari masu kama da kudin cizon) saka kaikayi ba. A kasashen Kudancin Amurka, irinsu Meziko, kudin cizo za su iya yada kwayoyin cuta na trypanosoma masu sa ciwon sammore da zai iya kama mutum da dabba, wanda mu kuma a nan kudan tsando ne ke yadawa.
Idan mutum ya ga kudin cizo a dakinsa, to kamata ya yi ya kwashe kayan shimfidarsa duka ya jika a ruwan zafi, kafin a wanke a shanya a rana. Wadanda suke da girma kuma a kai wa kwararrun masu wanki a yi masu bayani. Sa’annan sai a samu maganin feshi na kwari a feshe dakin tas, a jawo kofa a rufe har sai ya sarara.
Ni idan ina karatu sai na tura takardar gaba nake gani sosai. Ko raunin ido ne haka?
Daga Aliyu A. da Jamila danmaliki
Amsa: kwarai kuwa matsalar raunin ido ce. Gilashin likita wato tubarau medical, wanda sai an auna idon ake zana shi, zai taimaka sosai wajen sassaita matsalar.
Wai saka gurji wato cucumber a kan ido na kara wa idon lafiya ne?
Daga Ibrahim Sani
Amsa: A’a, masu dora gurji a ido ba idon suke sa wa ba, fatar gefen idon suke kokarin kara wa lafiya. Ka san gurji na da sinadarai masu kara wa fata lafiya da armashi, amma ko yaya aka yi amfani da shi zai wadatar, wato ko ci aka yi a abinci ko a dora a fuska na tsawon lokaci, duk za a iya samun amfanin.
Ni idan na gaisa da mutane hannu-da-hannu sukan ce hannuna da dimi. Ko matsala ce wannan?
Daga danladi, dambatta
Amsa: A’a, ba wata matsala, dimin jiki ne kawai. Ai dama dimin jikin wasu ya fi na wasu, mata sun fi maza dimin jiki saboda sinadaran estrogen, a mazan ma musamman a mutane masu kiba, dimin jikinsu yakan fi na marasa kiba, saboda sinadaran kitse su ma sukan samar da dimin jiki. Wannan shi ya sa kuma masu kiba suka fi sauran mutane jin zafi da yawan zufa.
Da gaske ne za a iya daukar cuta mai karya garkuwar jiki daga kayan aski ko na yanke kunba?
Daga U Show
Amsa: E, da gaske ne. Idan aka yi wa mai dauke da wannan cutar aski ko yankan kunba, sai kuma aka zo aka yi wa wani mai lafiya amfani da su kafin a tafasa ko kona su kayan aikin da wutar lighter, akwai babban hadarin kamuwa. Ba ciwo mai karya garkuwar jiki kadai ba, har da kwayoyin cutar ciwon hanta na Hepatitis B za su iya buya a kan kayan kaifi idan ba a daukar matakan tsabtace su a kodayaushe.
Ina yawan jin zafi da sanyi. Na je asibiti an yi mani gwaje-gwaje, an ce typhoid da maleriya ne, an yi mani karin ruwa da allurori, an kuma ba ni magunguna amma dai har yanzu ban gane wa jikin ba. Wannan wace irin matsala ce?
Daga Musa T.
Amsa: E, ga shi nan sun fada maka abubuwan da ke damunka. Haka za ka daure ka yi ta shan magani yadda suka tsara maka har su tafi. In an gama shan magani a kara gwaji a gani ko sun mutu ko suna jinin naka har yanzu.
Idan ina gudu sai na rika jin naman cikina dama ko hagu suna rikewa, wurin yana kumburowa. Idan na tsaya sai ya koma. Wace irin matsala ce wannan?
Daga Aminu Sa’ad, Kano
Amsa: Ba za a iya cewa takamaimai wace irin matsala ba ce sai an duba daidai wurin yayin da kake gudun. A asibiti, likita zai iya sa wa ka dan yi tsalle ya gani ko mene ne, inda zai tantance ko tsoka ce ko kari ko kaba ko ma wani abu daban.
Ni ma ina shan wata kwaya na kasa dainawa. Ga shi za a kira ni aikin soja. Zan iya samun matsala wajen atisaye?
Daga Sani, Abuja
Amsa: E, zai iya ba ka matsala, domin da wuya ka samu kwayar a wurin atisayen, wanda hakan kuma zai iya jefa ka cikin rashin lafiya. Don haka yana da kyau tun kafin a kira ku, ka samu ka je babban asibiti bangaren kwakwalwa, a dan kwantar da kai ana ba ka magungunan da kwakwalwarka za ta rika amfani da su kafin ta saba da rashin kwayar. Idan aka ga za ka iya rayuwa ba kwayar, a sallame ka ka tafi.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited