Gyara jikinki da koren ganyen shayi
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Gyara jikinki da koren ganyen shayi

Koren ganyen shayi na da amfani a jikinmu, domin shansa na kara lafiya da kuma kara gautsin fata. Za a iya shafa ganyen shayin a fuska.

Koren ganyen shayi na kare fata daga saurin tsufa. Bayan haka, yana kuma kare jikinmu daga cututtuka da dama. Yawan shan koren ganyen shayi na sanya a ga mutum kamar saurayi ko budurwa. alhali kuwa ya hada shekaru. Hanyoyi da za’a iya amfani da koriyar ganyen shayi.
• Za a iya amfani da koren ganyen shayi a fuska;
 A kan sanya wannan ganyen a mayuka da dama na shafawa. Domin ganyen na kunshe da sinadaran bitamin C da A da kuma E. Amfani da ganyen na rage maikon fuska, kuma fuskar ta yi santsi, yadda ko alamar kuraje ba za a ji ba. Za a samo mayonnaise sai a diba cokula uku daga shi. Sannan dakakken koren ganyen shayi. Za a rika shafa a fuska ban da gefen idanu. Sai a kykle shi na tsawon mintuna 20 sai a wanke da ruwan dumi.
• Amfani da koriyar ganyen shayi na rage warin numfashi;
A tafasa ganyen shayi. Bayan haka, sai a jira na tsawon mintuna 30. Sai a rinka amfani da shi wajen wanke baki. Yin hakan na hana dauda zama a kan hakori. Kuma zai kare bakin daga wari.
Shan shayin na rage kiba; za a  iya shan shayi safe da yamma domin rage maikon jiki.
• Koren shayi na rage tumbi ga macen da ta taba haihuwa da wadda ba ta taba haihuwa ba;
Shan ganyen shayi mara suga a kalla sau biyar a rana na matukar rage tumbi ga mata, musamman ma macen da ta taba haihuwa. Gwara a gyara tunda ba a kwalliya da tumbi. Yana da kyau a jure na tsawon watanni biyar za a yi matukar mamakin yadda tumbi zai shanye.
• Ganyen shayi na magance ciwon ido;
A sanya ganyen shayi a gidan sanyi na tsawon mintuna biyar, sannan a rika dorawa a kan idon har sai ya narke. Yana rage ciwon ido mai zafin nan da nan.
Yana gyara fuska;
• A samu koren ganyen shayi, sannan a zuba burbudin a cikin zuma, sai a rika shafawa a fuska na tsawon mintuna 20 a kalla sau biyu a rana; safe da yamma. Yin hakan na magance fesowar kurajen fuska.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited