Inganta kwalliyarki ta hanyar rage tumbi
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Inganta kwalliyarki ta hanyar rage tumbi

Barkanmu da sake saduwa da ku a wannan filin namu na kwalliya. Lallai kwalliya ba ta tsaya a yadda ake shafa hoda ko iya sanya jan baki ba. Domin akwai abubuwa da dama, wadanda mace ya kamata ta yi, domin inganta kwalliyarta.

Mace in ta cika yawan kiba ko tayi kwalliyar ba ta cika haskawa ba, domin su kumatu sun cike fuska, sai a ganta kamar wadda ta tashi daga jinya ko bacci. Don haka ina mai bai wa mata shawara wajen kulawa da kansu.
• Zuma na matukar taimakawa wajen rage kiba ko tumbi domin yana dauke da sinadaran da ke taimakawa wajen narkar da abinci a ciki da wuri; a samu kofi daya na ruwan zafi sannan a zuba zuma da ruwan lemun tsami da kirfa sannan a rika sha safe da yamma za a ga canji.
• Ruwan lemun tsami na rage kibar jiki ko tumbi, domin yana dauke da sinadaran narkar da maikon cikin jiki da kuma na tumbi;  a samu ruwa a kofi sannan a matsa ruwan lemun tsami da zuma, sai a rika sha kullum da safe kafin a ci komai. Yana matukar taimakawa wajen rage tumbi da kiba.
• Kirfa (za a iya samu wajen masu sayar da kayan kamshi ko gargajiya) na taimakawa wajen rage kibar da ke kwankwaso da na hakarkari, kuma yana rage sigar da ke cikin jini. Siga na sanya kiba. Don haka dole ne a samu abin da zai rage ta; a samu kofin ruwan zafi sannan a zuba kirfa da kuma zuma, sai a rika sha da sassafe kafin a karya.  Bayan an gama cin abincin dare da mintuna 45 sai a sha.
• Koren ganyen shayi; shan shayin mai koren ganye na taimakawa wajen rage tumbi; a samu gora sai a zuba ganyen, sannan a yayyanka gurji da ruwan lemun tsami a rufe su kwana, sai a sha da sassafe kafin a ci komai. Ko kuma a  yawaita shan ganyen shayin kamar sau biyar a rana.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited