Magance tabon fatarki 2
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Magance tabon fatarki 2

Mutane da dama na fuskantar kalubalen tabon fata da kuma yadda za su magance su. Ga shi nan a yau zan cika muku alkawuranku, kamar yadda na fada yau na kawo muku yadda za a magance wadannan matsalolin.  Akwai abubuwa da dama da ya kamata a yi amfani da su. Amma ina son masu karatu su san cewa an fi son a yi amfani da daya daga cikin hadin a jiki. Ka da a cakuda komai. Idan aka cakuda, ba za a samu biyan bukata ba.
Itacen sandalwood da zuma. A nika itacen sandalwood, sannan a zuba zuma, a cakuda su sai a shafa a fuska ko a inda akwai tabo bayan mintuna 30, sannan a wanke da ruwan dumi. Itacen sandalwood na tayifar da tabo sosai, kuma yana taimakawa wajen haskaka fata. Yawan shafa zuma zalla a tabo na batar da shi. Amma sai an yi hakuri domin sauki sai a hankali. Za a iya amfani da wannan hadin na tsawon watanni uku kafin samun biyan bukata.
kwallon dabino da man kwakwa wannan hadin na taimakawa wajen batar da tabo, musamman wanda aka samu daga kunar wuta ko ruwan zafi. A gasa kwallon dabino sai a nika shi, sannan a hada da man kwakwa. Sai a shafa hadi a inda ake bukata. Za a iya samun kamar kwallon dabino 10 a wannan hadin.
Zuma da lemun tsami
A samu zuma sannan a zuba ruwan lemun tsami a rika gogawa a inda tabon yake a kullum kamar sau biyu a rana. A shafa a wajen tabo kamar  na tsawon mintuna 30 sannan a wanke da ruwan dumi. Ana so a yi ta maimaita hakan na tsawon watanni uku kafin a bari.
 Man ‘Castor’
A samu man castor, sannan ana hadata da zuma da zaitun sai a rika shafawa a inda akwai tabon a kowane awa na tsawon mintuna 30 sannan a wanke. Yana da kyau a rika amfani da wannan na a kalla watanni uku sannan za a fara ganin canji.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited