Kwalliya a cikin mintuna biyar kacal
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Kwalliya a cikin mintuna biyar kacal

Gaskiya idan ana zancen kwalliya, kayan kwalliya mai tsada ne ya fi dacewa da kowace fuska. Yana da kyau a zabi launin jan baki da ya dace da baki.

Ba a cika son maka kowane irin launin jan baki ba. Haka kuma launin hodar da ta dace da fata da kuma irin launin kwallin da za a gyara gira da ita da sauransu. A yau na kawo muku yadda za a yi kwalliya a cikin mintuna biyar ba tare da bata lokaci ba.
•Jan launi ya fi dacewa da kowane irin baki, don haka  idan za a zabi launin jan baki, a zabi mai launin sosai. Kuma ina son a san cewa, jan launin ma ya bambanta. Idan ke baka ce, sai ki zabi ja, amma ba mai haske sosai ba. Domin fitar da kwalliyarki.
•Kada a manta irin ‘eye shadow’ abin zanen gira da za a shafa a kan fatar ido. Ya kamata launin ya kasance ya dace da launi tufafin da za a sanya bayan an gama kwalliya.
•Idan za’a shafa hoda, yakamata a san wani irin fata ake da ita. Idan ke mai gautsin fata ce, sai ki sami hoda mai maiko (fandesho) wanda ya dace da launin fatarki. In  baki da gaustin fata, sai ki shafa hoda haka wanda ta dace da fatarki.
•Adon gira; launi mai ruwan kasa ya fi dacewa da kowace irin fata. Amma idan ke baka sosai ce, za ki iya amfani da gazal (jagira) baki, domin fitar da kyawun girarki. Idan kuwa ke ruwan tarwada ce ko fara, za ki iya amfani da gazal (gazar) mai launin ruwan kasa a gira.
•Kayan sawa; yana da kyau a gane irin launin tufafin da ya dace da kowace irin fata; idan ke baka ce sai ki yawaita amfani da kaya wadanda launinsu ke da haske. Haka zalika idan ke fara ce sanya kayan da launinsu ke da duhu, don su suka fi dacewa.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited