Yadda za ki rage kiban jikinki a kwana qanqani
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Yadda za ki rage kiban jikinki a kwana qanqani

Kiba na daya daga cikin ababen da ke rage kyawun mace. Idan kiba ta yi yawa sai a ga ta shanye karan hancin. Idanuwan kuma su zama kanana, sannan taya ni muni duk su bayyano.

Sannan ba kowace riga za ta dace da jikin ba. Don haka ne a yau na kawo muku ababen da za a ci domin rage kiba. A sha karatu lafiya.
•A rage cin duk wani abu da ya kunshi alkama ko aka yi ta da alkama da safe. Domin ba karamar kara tunbi take ba.
•Yana da kyau a yawaita cin ‘ya’yan itatuwa, domin yawaita cinsu na rage kibar jiki, musamman ma na tunbi. Kuma suna inganta lafiyar jiki sosai.
• A rage cin naman shanu, tunda yawan cinsu na sanya kiba. Don haka sai a samu naman kaza ko a yawaita cin kifi.
•A yawaita yin abinci da man zaitun, domin yana rage maikon jiki da kuma rage duk kowane maikon da ake samu a nama ko abinci.
•A yawaita cin kwai a kowace safiya idan an zo karyawa, amma kwan kada ya wuce daya.
•A samu latas ko kabeji a yawaita kada kwadonsa, domin cinta a matsayin abincin rana. A samu ko rama ko zogale, sai a yawaita cinsu da tumatir da albasa domin rage kiba.
•A tabbata an tsayar da cin abinci mai nauyi a kowane karfe biyar na yamma. Sai kuma shayi.
•A daina cin nau’ukan abinci masu nauyi da yamma, domin shi ne ummul aba’isin da ke janyo tunbi da kasala da kuma kiba.
•Kada a kwanta da zarar an gama cin abinci mai nauyi. A tsaya na tsawon awa daya bayan an ci abinci kafin a kwanta. Kwanciya dab da an gama cin abinci na haifar da cuta da kuma dada kiba.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited