Rashin hanyoyi ne matsalarmu a garin Kwara – Inji Ardon Kwara
Friday 28 July 2017     4 Zulki'da 1438

Aminiya

A+ A A-

Rashin hanyoyi ne matsalarmu a garin Kwara – Inji Ardon Kwara

Ardon garin Kwara dake karamar Hukumar Kiana a Jihar Nasarawa alhaji Mohammed Jibrin yace a yanzu ana samun fahimtar juna a tsakanin Fulani, makiyaya da sauran kabilu manoma a yankin. Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya game da nasarori daya samu bayan nadinsa a matsayin sabon ardon garin Kwara wanda mai martaba sarkin Kwara alhaji Ibrahim Oboshi ya yi a kwanakin baya. Yace garin Kwara wanda daya ne daga cikin garuruwa da rigingimun manoma da fulani makiyaya suka shafa a kwanakin baya, a yanzu dai acewarsa an samu dawwamamman zaman lafiya tsakanin al’umarsa ta Fulani da sauran kabilun garin baki daya. Ya cigaba da cewa “Kaga abu na farko da nayi bayan mai martaba sarkin Kwara alhaji Ibrahim Oboshi ya nada min mukamin sabon ardon Kwara shine na tara al’ummana Fulani inda na ja hankalinsu game da mahimmancin zaman lafiya tsakaninsu da sauran kabilun dake yankin. Bayan wannan na kuma gana da shugabannin wadannan al’ummomi inda muke zama akai-akai muna samo hanyoyin warware duk wani sabani da ake samu tsakanin mu. Kuma alhamdullillah hakarmu na cimma ruwa a wannan bangare.” Alhaji Jibrin ya kuma bayyana cewa babban matsala da suke fuskanta a yankinsu a yanzu shine rashin hanya mai kyau. Ya ce musamman a wannan lokacin damuna da ake ciki dazarar an yi ruwa hanyoyin yankin ba a iya yin amfani dasu. kasancewa galibinsu manoma ne da makiyaya sannan ya bukaci gwamnatin jihar ta dubesu da idan rahama a wannan bangare. Ya kuma bayyana cewa a halin yanzu ardodi da takwarorinsu sauran shugabannin al’ummomin yankunan basa samun albashi ko wani tallafi daga gun gwamnati inda ya bukaci gwamnati ta rika tallafa musu don basu damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. Daganan ya shawarci al’ummarsa Fulani da manoma a yankin baki daya da su gujewa daukar doka a hannunsu, domin a samu daurewar zaman lafiya daya dawo yankin a yanzu.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited