Allah Ya yi wa Sani Gwarzo rasuwa
Friday 28 July 2017     4 Zulki'da 1438

Aminiya

A+ A A-

Allah Ya yi wa Sani Gwarzo rasuwa

A ranar Litinin da ta gabata ce Allah Ya yi wa shahararren dan jaridar nan kuma tsohon ma’aikacin gidan Rediyo da Talabijin a  gidan Rediyon Tarayya na Kaduna, Alhaji Sani Gwarzo rasuwa a gidansa da ke Kinkinau, Kaduna.
Marigayi Sani Gwarzo, wanda ya shahara a aikin jarida a kasar nan da kasashen waje, ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya. Marigayin ya rike mukamin Mukaddashin-Daraktan Shirye-Shirye na Gidan Rediyon Tarayya na Kaduna, kafin ya yi ritaya a shekarun baya. Har ila yau, ya yi aiki da kafafen watsa labarai na kasashen waje a lokacin rayuwarsa.
daruruwan jama’a ne suka samu halartar jana’izarsa a gidansa da ke Kinkinau, wadda aka yi misalin karfe biyu na rana, kafin a wuce da shi makwancinsa a makabartar da ke kan Titin bashama a Tudun Wada Kaduna. Tsofaffin abokan aikinsa da abokan arziki sun halarci janaza’izar tasa.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited