Ya nemi ma’aikata a Jihar Nasarawa su koyi hakuri da juriya
Friday 28 July 2017     4 Zulki'da 1438

Aminiya

A+ A A-

Ya nemi ma’aikata a Jihar Nasarawa su koyi hakuri da juriya

Kwamishinan Al’amuran kananan Hukumomi da Masarautun Gargagajiya na Jihar Nasarawa, Alhaji Aliyu Ahmad Tijjani, ya yi kira ga al’ummar Jihar Nasarawa, masamman ma’akatan kananan hukumomi tun daga shugabanninsu zuwa kananansu su kasance masu hakuri da duk yadda suka tsinci kansu, dangane da irin biyan kudin albashi na kashi-kashi da ake yi a jihar.
“Kudin albashi da ake ba ma’aikata kashi-kashi a jihar, ba laifi mahukunta ba ne. Hakan na faruwa dangane da irin kudin da ke zuwa mana daga sama, wanda dole ne a yi hakan domin kowa ya samu albashi. Amma idan har an ce za a ba da cikakken kudin, tabbas wadansu ba za su samu ba. Wannan hujja ce ta sa wannan gwamnati mai adalci ta yi tsarin bai wa kowa hakkinsa koda bai cika ba, domin Hausawa na cewa da babu gara ba dadi. Kuma abin da ya sa, muna samun karancin kudi daga sama, sakamakon karayar tattalin arzikin Najeriya. Da wannan ne nake kira ga ma’aikatan kananan hukumomi su kasance masu hakuri da juriya da fahimtar gwamnati, domin bayan wuya sai dadi,” inji shi.
A nasa bangaren, Shugaban kungiyar Shugabannin kananan Hukumomi (ALGON) ta Jihar Nasarawa Alhaji Suleiman Wambai, ya yi kira ga shugabannin kananan hukumomi 13 na jihar, su koyi akidar tsimi da tanadi, domin samun damar yi wa talakawa aiki da dan abin da suke samu daga kason da ke zuwa daga sama.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited