Alhaji Lili Gabari ya kwanta dama
Friday 28 July 2017     4 Zulki'da 1438

Aminiya

A+ A A-

Alhaji Lili Gabari ya kwanta dama

A ranar Talatar da ta gabata ce Allah Ya yi wa fitaccen dan siyasar nan, Alhaji Lili Gabari rasuwa a gidansa da ke Kano.
Marigayin ya rasu yana da shekara 86 a duniya, bayan ya yi fama da rashin lafiya na wani lokaci. Ya fara gwagwarmayar siyasa tun daga Jam’iyyar NEPU a Jamhuriyya ta Farko. A Jamhuriyya ta Biyu kuma ya fafata a  Jam’iyyar PRP, yayin da a wannan zubin siyasa har zuwa rasuwarsa mamba ne a Jam’iyyar PDP.
Marigayin ya taba zama dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Jahun da Aujara. Kuma ya taba zama Mai ba wa Gwamnan Jihar Kano, marigayi Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi shawara a kan al’amuran majalisa.
Tuni dai aka yi jana’zarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Da yake jawabi a kan rayuwar marigayin ta siyasa, abokin harkarsa a siyasa Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana shi da cewa yana daga cikin ’yan kalilan din ’yan siyasar da suka dauki nauyin Jami’iyyar NEPU da kudinsu. “Kasancewar shi dila ne na gyada, ya yi amfani da kudinsa wajen ba Jam’iyyar NEPU gudunmawa. Ya sadaukar da kansa da dukiyarsa a kan fitar da mutane daga cikin kangin bauta a kasar nan,” inji shi.
Alhaji Tanko Yakasai ya kara da cewa: “Rasuwar marigayin babban rashi ne ga siyasar kasar nan, wanda cike gurbinsa zai zama jan aiki a irin zamanin da muke ciki.”

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited