Makarantar Hayatil Islam ta yaye dalibai 49
Friday 28 July 2017     4 Zulki'da 1438

Aminiya

A+ A A-

Makarantar Hayatil Islam ta yaye dalibai 49

A makon da ya gataba ne makarantar Sheikh Lawal Abubakar, Madarasatu Hayatil Islam da ke Hayin Banki, karamar Hukumar Kaduna ta Arewa a Jihar Kaduna ta yaye dalibanta su 49, wadanda suka hada da yara 34 da matan aure 15.

A jawabin shugaban makarantar, Malam Ibrahim Abudllahi mai gyaran agogo, wanda mataimakinsa Malam Aliyu Usman kari ya wakilta, ya nuna cewa wannan shi ne karo na 11 da makarantar ke saukar da dalibai yara sannan kuma karo na 4 a bangaren karatun matan aure.
Aminiya ta samu zantawa da wasu daga cikin malaman makarantar. Malam Ishak Ango ya nuna farin cikinsa da ganin wannan ranar. “Gaskiya ina matukar murna da ganin wannan ranar, domin a ce matan aure guda 15 sun sauke Alkur’ani mai girma, ai ka ga al’umma za ta gyaru sosai. Ina addu’ar Allah Ya sanya wa karatun albarka kuma Allah Ya sa karatun ya amfane su a duniya da lahira kuma Allah Ya sa su ma su koyar da wasu.” Inji shi.
Shi Malam Mukhtar Abdullahi, wanda ya saukar da bangaren yara cewa ya yi: “Wannan babbar rana ce ga tarihin wannan makaranta. Ina taya wadannan daliban murna sosai kuma ina fata Allah Ya sa karatun ya amfane su a duniya da lahira.”
Daga cikin daliban da Aminiya ta zanta da su, akwai Zainab Shehu Goma wacce ta sauke a bangaren matan aure, inda ta nuna cewa tana farin ciki sosai da ganin wannan rana da Allah Ya sa ta sauke Alkur’ani mai girma. Ta ce tana godiya ga Allah, sannan kuma ta ce tana fata Allah Ya sa wa karatun da suka yi albarka.
Shi ma a nasa jawabin, shugaban daliban makarantar a sashen yara, Abubakar Umar wanda aka fi dani da Amir, ya nuna cewa a madadin shi kansa da sauran daliban da suka yi sauka, suna godiya ga Allah da malamansu da suka saukar da su.
Daga cikin wadanda suka halarci taron, sun hada da dan majalisa mai wakiltar mazabar Kawo a Majalisar Jihar Kaduna, Alhaji Aliyu Haruna Chakis da Alhaji Al’amin Dabo wanda ake kira Bosa, tsohon Kansila Alhaji Gambo Abdullahi Acro, iyayen dalaibai, tsofaffain daliban makantar, abokanan arziki da sauran mutane wadanda suka cika filin walimar domin taya wadanda suke walimar murna.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited