An gano sabon salon damfarar mata a Jigawa 1
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

An gano sabon salon damfarar mata a Jigawa 1

Kwamashiniyar Mata a Jihar Jigawa, Hajiya Ladi Ibrahim ta nemi hadin kan ’yan sanda da bincika domin gano yadda wasu bata-gari ke yawo da sunanta a jihar suna amsar Naira dubu uku a hannun mata, da sunan za a yi masu rijistar samun bashi daga Gwamnatin Tarayya.

Kamar yadda bayanai suka nuna, al’amarin na ’yan damfara ya kai wani mataki, inda da rahotannin suka isa kunnen kwamashiniyar ta mata da jin dadin jama’a. Ta ce ita dai kam ba ta tura kowa ba kuma ofishinta ba ya da masaniya a kan harkar, ba ta kuma tura kowa ya amshi kudi a wajan mata ba, don haka duk wadda ta ba wani kudi ko waye, ya ba su kudinsu.
Ta kuma umurci matan da aka damfara da su sanar da jami’an tsaro, domin a yi masa hukunci. Ta kuma bukaci matan da su tona asirin duk wanda ya amshi kudi a wajansu komai matsayinsa.
“A iyakacin sanina, ma’aikatana ba za su aikata irin wancan al’amarin da wadancan bata-garin suke aikatawa ba. Ina neman hadin kan jami’an tsaro da ke cikin kananan hukumomin jihar nan da su sanya ido wajen kame duk wanda aka samu suna amsar sunayan jama’a, suna karbar Naira 3000 da sunan za su yi wa matan rijista.” Inji ta.
Ta kara da cewa za ta rubuta takarda zuwa ofishin duk jami’an tsaro na jihar, domin daukar mataki a kan wadanda sukey in wannan rashin kirki. Ta ce ba za ta saurara wa duk wanda aka samu yana yi wa gwamnatin jihar zagon kasa ba.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited