An ci tarar mashaya giya Naira dubu 320 a Jigawa
Friday 28 July 2017     4 Zulki'da 1438

Aminiya

A+ A A-

An ci tarar mashaya giya Naira dubu 320 a Jigawa

Kotun Shariar Musulunci da ke Kazaure a Jihar Jigawa, ta yanke wa mutane 22 (maza 10, mata 12) hukuncin biyan tarar Naira dubu 320, bisa laifin kwankwadar barasa.

Su dai wadannan mutane, kowanne daga cikinsu zai biya tarar Naira dubu 20 ne, kamar yadda Mai Shari’a, Mamuda Tahir ya hukunta.
Tun da farko dai, Rundunar Hisba ta Jihar Jigawa ce ta gurfanar da mashayan, inda bayan yanke hukuncin, alkalin ya zartar masu da hukuncin biyan tara ba tare da zabi ba. Haka kuma ya ba da umarnin a rufe gidajen giyar da aka kama su suna kwankwadar giyar na tsawan wata takwas.
Haka kuma, kotun ta rufe wani gidan giyar da ake wa lakabi da ‘Gidan Kola’ saboda samun mai gidan da laifin karya dokar kotu, wacce ta hana shi sayar da giya.
Haka kuma a karamar Hukumar Gwiwa, wata kotun ce a karkashin Mai Shari’a Usman Alkali ta yi wa wasu mutane su shida bulala tamanin-tamanin a gaban jama’a saboda samun su da laifin shan giya a wani gidan burkutu. Cikin wadanda aka kama, hard a wata mata, wacce kotu ta samu tana fama da rashin lafiya, don haka aka umurce ta da ta biya tarar Naira dubu bakwai, maimakon bulalar da za a yi mata.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited