Sai mun koma ga Allah kafin mu fita daga matsin rayuwa - Farfesa Cika Umar
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Sai mun koma ga Allah kafin mu fita daga matsin rayuwa - Farfesa Cika Umar

Farfesa Cika Umar Aliyu ya bayyana cewa matsin tattalin arzikin day a addabi al’ummar Najeriya ba zai gushe ba, har sai an koma wa tsarin Allah.

“Matukar Gwamnatin Najeriya ta bi hanyoyin da musulunci ya samar kan tattalin arziki, za a fita daga cikin
matsin rayuwa da ake fama da shi.
“Tattalin arzikin Najeriya na ’yan Jari-hujja ne da aka karbo daga Turawan Yamma, aka yi masa kwaskwarima a shekarar 1986, aka ci gaba da bin sa har zuwa wannan lokacin da tsarin tattalin arzikinmu ya shiga matsanancin hali; talaka na ji a jikinsa fiye da sauran lokutta. Don haka matukar Gwamnatin Najeriya ba ta bi hanyoyin da Musulunci ya samar kan tattalin arziki ba, ba za a fita daga cikin matsin rayuwa da ake fama da shi ba.”
Farfesa ne ya yi wadannan kalamai a wurin taron kasa da aka gabatar a makarantar haddar Alkur’ani da ilmi ta Sarkin Musulmi Maccido da Majalisar Malaman Addinin Musulunci ta Najeriya reshen Jihar Sakkwato ta shirya a birnin, domin tattauna hanyoyin da za a bi a farfado da tattalin arzikin Najeriya da ke cikin matsala.
Ya ci gaba da cewa, tattalin arzikin Najeriya a bangaren harkar kudi na dabaibaye ne da harkar ruwa, kan haka yake habaka a wurin samu amma da an zo wurin amfani sai ka ga komai ya rushe, wato yakan yi kumfar omo ne. Da za a shigo da tsarin Musulunci a harkar tu’ammali da kudi da kasar nan ta samu wani irin tagomashi, tattalin arziki zai farfado a bangarori daban-daban; za a samu tsayyayen abin dogaro kan harkar kudi.
Haka ma ya kara da cewa, adalci a wurin rabon arzikin kasa da kulawa da harkar zakka, gwamnati a kowane mataki ta kula da talakkawanta, a samar masu da kayan more rayuwa, a samu adalci a tafiyar da gwamnati kamar yadda addini ya kwadaitar na kula hakkin dan kasa. Kar a bari Jari-hujja ta shiga gaba a gwamnati, domin tana karya mulkin adalci. Kamata ya yi gwamnati ta mamaye komai, kar ta ba masu zaman kansu a harkar kasuwanci ikon cin gashin kai na gaba daya. Hakan ke sanya komai ya baci, kasa ta shiga halin kunci, talaka ya rasa wurin dafawa, rana zafi, inuwa kuna.
Mai martaba Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, a jawabinsa ya yi kira ga malamai da su daina jayayya da junansu matukar ba son girma da kudi ne ya mamaye zuciyarsu ba. “Malamai ne ya kamata su fada wa gwamnati gaskiya, domin ta gyara kuma a cikin hikima da ladabi; domin ya kamata malamai su daina sanya fitinannen malami a cikinsu ya yi wa’azi, don ba a samun fahimta da tarnaki tun da ilmi ba gadonsa ake yi ba.” Inji shi.
Da ya juya kan aikin masarauta, ya ce sun yi kokarin fassara littattafai fiye da 300 na Daular Usmaniyya a harsuna daban-daban, don a samar da ilmi a kasar nan.
Shugaban malamai na majalisar malamai ta Sakkwato, Malam Umar Muhammad Bagarawa ya gabatar da takarda mai taken tattalin arzikin Najeriya. Haka ma Gwamnatin Jihar Sakkwato ta nuna jin dadinta kan wannan aikin da bayar da taimako na miliyan 5 ta hannun Sakataren Gwamnati.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited