Dalibai 14 sun yi sauka bayan kowa ya rubuta Alkur’ani da kansa
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Dalibai 14 sun yi sauka bayan kowa ya rubuta Alkur’ani da kansa

Ranar Lahadin nan da ta gabata, Makarantar Islamiyya ta Ta’alimulsunna Waliyadul kur’an da ke titin Nasara a Hayin Rigasa Kaduna cikin karamar Hukumar Igabi ta yaye dalibanta 14.

daliban da aka yaye maza bakwai ne mata bakwai a karo na uku. A cewar hukumar makarantar dukkan daliban sai da suka rubuta Alkur’ani da hannunsu kafin aka sauke su, sabanin yadda wasu makarantun suke sauka, inda za a bai wa dalibi wasu ayoyoyi ya karanta.
Da yake bayani a wajen bikin yaye daliban, wanda aka yi a harabar makarantar, Babban Limamin Masallacin Juma’a da ke Hayin Malam Bello, Shaikh Abdulhadi Aliyu Daura, jan hankalin Musulmi ya yi da su rika taimaka wa addinin Allah a duk inda suke. A cewarsa, akwai bukatar Musulmi su taimaka wa makarantun Islamiyya domin akwai kokari da kasashen Turawa ke yi wajen ganin sun rusa irin wadannan makaramtu.
Ya kuma ja hankalin Musulmi da su taimaka wa makarantar Ta’alimulsunna waliyadul kur’an, domin ci gaba da ginin ajujuwa da take a yi. “Muna yi wa malaminmu Marigayi Bello Aladamawi fatan Allah Ya jikansa, domin shi ne kafin rasuwarsa ya ba da wasiyyar a yi amfani da kashi daya na dukiyarsa wajen yin aikin alheri da shi kuma cikin yardar Allah da dukiyarsa aka samu gina wasu ajujuwa a wannan makaranta.
“Wannan ya sa muke kara jan hankalin Musulmi da su daure suna cire wani abu daga cikin dukiyarsu wajen taimaka wa addinin Allah. Wannan makaranta na matukar neman tallafi da fatan Allah zai kawo mana wadanda za su taimaka a kammala ta,” inji shi.
daya daga cikin iyaye mata a makarantar, Hajiya Maryam Abdullahi Ahmad Rufai, ta bayyana cewa daliban makarantar suna samun tarbiyya irin ta addinin Musulunci. Ta kuma yaba wa kokarin malamansu bisa kokari da suke yi wajen karantar da yaran.
Tsohon shugaban dalibai na makarantar, Ali S. Nuhu, wanda yana cikin ’yan kwamitin shiryawa na makarantar ya yi kira ga iyayen yara da su mayar da hankali kan karatun ’ya’yansu, inda ya ce akwai bukatar iyaye su rika biyan kudin makaranta a kan lokaci. Ya kuma yaba wa malaman makaratanr bisa kokari da suka yi wajen ganin kowane dalibi sai da ya rubuta Alkur’ani da hannunsa kafin aka yaye shi.f

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited