Ya daddatsa abokin aikinsa ya cusa a buhu
Friday 28 July 2017     4 Zulki'da 1438

Aminiya

A+ A A-

Ya daddatsa abokin aikinsa ya cusa a buhu

Rundunar ’yan sanda a Jihar Legas ta kama wani matashi, Haruna Abubakar dan shekara 28, wanda ake zargi ya daddatsa abokin aikinsa ya jefar da shi a cikin daji.

Kamar yadda Mujallar The News ta ruwaito, mutumin da ake zargi da aikata laifin, shi da abokinsa suna aiki ne a wata gona da ke Ibeju Lekki, inda shi wanda ake tuhuma da aikata laifin ke aikin gadi kuma wanda aka yi wa kisan gillar yana kiwon shanu.
A ranar Asabar da ta gabata, Haruna Abubakar ya samu sabani da abokin aikinsa, har ta kai ga sun gwabza fada. Suna cikin fadan ne sai wanda ake zargi ya kai wa marigayin hari da adda, inda ya daddatsa shi gunduwa-gunduwa, sannan ya cusa a cikin buhu, ya kai daji ya zubar.
dan uwan marigayin, Adamu, shi ya kai kuka a wajen ’yan sanda cewa dan uwansa ya bace, bayan da ya ga bai dawo daga wajen aiki ba a wannan rana.
Da ’yan sanda suka ga wata alama, sai suka yi ta binciken wanda ake zargi, har ta kai ga ya amsa laifin kisan, inda daga bisani ya kai su wurin da ya daddatsa abokin aikin nasa.
Kwamishinan ’yan sanda, CP Fatai Owoseni ya bayar da umarnin mayar binciken al’amarin zuwa sashen bincike na na musamman (SCID) da ke Panti a Yaba, Legas; inda za a karkare bincike sannan a gurfanar da mai laifin a gaban kotu.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited