Za mu ci gaba da bullo da hanyoyin dakile miyagun laifuka – Shugaban ‘yan sanda
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Za mu ci gaba da bullo da hanyoyin dakile miyagun laifuka – Shugaban ‘yan sanda

Babban sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya Idris K. Abubakar ya ce rundunar za ta ci gaba da bullo da sabbin hanyoyi na dakile aikata miyagun laifuka da suka hada da satar mutane ta yadda al’umar kasa za su kara samun zaman lafiya da kwanciyar hankali kamar yadda ake bukata. 

Ya yi wannan tsokaci ne yayin da ya kaddamar da sashen yaki da masu garkuwa da mutane wanda gwamnatin jihar kano ta gina don kakkabe ayyukan masu satar mutane a jihar, inda ya kara da cewa abin da gwamnan kano ta yi ya dace kwarai idan aka dubi irin halin da ake ciki na yawan satar mutane da na garkuwa da su domin neman kudin fansa.
Alhaji Ibrahim Idris ya kuma karbi motoci na sintiri guda 25 da gwamnatin kano ta samar a kokarinta na tallafa wa kokarin da hukumomin tsaro keyi na kawar da laifuka a fadin kasa, tare da jaddada cewa rundunar ‘yan sandan kasar nan za ta kara himma wajen kare rayuka da dukiyoyin al’uma kamar yadda abin yake cikin manufofin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited