Yadda karuwai suka addabi manyan titunan garin Bauchi
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Yadda karuwai suka addabi manyan titunan garin Bauchi

Kamar yadda ake fama da matsalar shan miyagun kwayoyi a tsakanin matasan kasar nan, yanzu kuma a cikin garin Bauchi daya, daga cikin manyan matsalolin suka addabi manyan titunan cikin fadar jihar, ita ce matsalar karuwar sana’ar karuwanci a tsakanin kananan yara mata.

Binciken Aminiya ya tabbatar da cewa ’yan mata ’yan 14, 16, zuwa 18, sun dauki karuwanci a matsayin wata babbar hanyar samun kudin shiga a garin Bauchi.
A Shekarun baya, ana samun karuwai ne a cikin unguwar Tudun Wadan dan Iya, da ake kira da bayan gari amma yanzu akwai wasu manyan titunan cikin garin Bauchi da karuwanci ya samu wurin zama, inda tun daga karfe shida na yamma har zuwa karfe 10 na dare ake gudanar da shi. Za ka samu ’yan mata suna tsaye a bakin titi suna jiran wadanda za su dauke su, domin yin lalata da su.
Kadan daga cikin manyan titunan da karuwai suke cin karensu babu babbaka, sun hada da titin da ke kusa da Babban Bankin Najeriya (CBN), daura da Bankin Sterling. Kullum za ka samu ’yan mata a tsaye a bakin hanya suna jiran wadanda za su dauke su. Haka ma lamarin yake a titin da ke daura da Kasuwar Laushi.
Mutum na zuwa kofar shiga ‘Multifafos’ haka zai samu ’yan mata ’yan kasa da shekara 20 suna jira. Wasu daga cikinsu matasa ne masu baburan da ake kira roba-roba suke daukar su, daga nan sai su karbi daki a otel domin aikata fasikanci da ’yan matan.
Kamar yadda wani matashi ya sanar da Aminiya, ya ce: “Idan mutum ya je bayan gidan Wazirin Bauchi, Alhaji Muhammadu Bello zai samu tarin ’yan mata, wadanda suka fito daga jihohi daban-daban na kasar nan, a kofar otel din Salamah, nan ma suna jiran kwastomomi.” Lokacin da wakilin Aminiya ya ziyarci wajen da misalin karfe 8:20 na dare, yana tsayawa da motarsa sai wata yarinya ta bude kofar motar ta shiga. Sai ta ce masa “Alhaji, wane otel za mu je yanzu?” Sai ya ce mata shi dan jarida ne, yana gudanar da wani bincike ne. Ya ce mata, “ko za ki fada mini sunanki na asali?”
Ta ce masa sunanta Sakina kuma ita ’yar asalin Jamhuriyar Kamaru ce. “Na shafe sama da wata biyu da zuwa Bauchi, ina zaune ne a unguwar Tudun Wadan dan Iya da ake kira bayan gari. Wajen wata kawata ce ta ce mini na zo kofar Salama, ana samun kwastomomi a kowace rana,” inji Sakina.
Ta kammala bayaninta da cewa: “Iya abin da zan fada maka ke nan, sai anjima Malam, kada ka bata mini lokaci; domin na fito neman kudi ne, ba na zo magana da dan jarida ba ne.”
Binciken Aminiya ya gano cewa, yanzu haka akwai wani babban otel a Bauchi (an sakaya sunansa), wanda mafi yawan matan da ake kai wa wajen, matan aure ne da zawarawa. An yi zargin cewa wani babban mutum ne a jihar ya gina shi.
A can baya, Hukumar Shari’ar Musulunci ta jiha ta sha kai samame wasu daga cikin otal-otal din da ake zargin ana lalata da kananan yara.
Akwai wadanda suke cewa matukar gwamnati tana so a rage masu kamuwa da cutar kanjamau, wajibi ne a sa ido game da abubuwan da ke faruwa a otel-otel din da ke cikin garin Bauchi.
Binciken da wakilinmu ya gudanar, ya gano wasu kananan otel-otel, inda suke ba da hayar daki na awa daya a kan kudi Naira 400 ko 500 ko 800, inda mutum zai je da buduwarsa a ba shi daki na dan wani lokaci. Mafi yawan ’yan matan da ake kai su gidajen badalar, ana dauko su ne daga bakin hanya; wasu kuma daga gidan iyayensu, kafin daga bisani idan an gama sharholiya a koma gida.
Da yake zantawa da wakilin Aminiya a ofishinsa da ke Bauchi game da wannan matsala ta karuwanci da ke neman zamowa ruwan dare a cikin garin Bauchi, Alhaji Bala Ahmed, wanda shi ne Sakataren Hukumar Shari’ar Musulunci ta Jihar Bauchi; ya bayyana cewa tabbas jami’an hukumar Hisba sun sha cafke kananan yara ’yan mata, wadanda suka fito yawon karuwanci da da dare. “Mafi yawan ’yan mata da aka kama, wasu sun fito ne daga jihohin Borno, Yobe, Gombe, Kano da sauran manyan garuruwa. Daga cikin wadanda hukumar ta sha kamawa, akwai matan aure, Zawarawa, ’yan mata da kuma wasu da sun manyanta amma har yanzu suna ci gaba da karuwanci a Bauchi.
“Tabbas ’yan Hisba sun kama mata da yawa a kofar otal din Salamah da ke bayan gidan Bello Kirfi kuma har yanzu hukumar tana ci gaba da kai samame wuraren da ake aikata badala a Bauchi. Al’amuran ne suka yi yawa a Bauchi don haka wasu ke ganin kamar hukumar ba ta aiki yadda ya kamata.” Inji Sakataren, yayin da yake karin bayani ga Aminiya.
Daga bisani Bala Ahmed ya kara da cewa tabbas hukumar tana sane da wuraren da ake aikata shaye-shaye da lalata da mata kuma yana rokon al’ummar Jihar Bauchi da su ci gaba da ba da bayanan sirri ga Hukumar Shari’ar Musulunci ta Bauchi, domin ta haka hukumar za ta samu damar kawar da wuraren da ake aikata miyagun laifuffuka.
Da yake amsa tambayoyin wakilin Aminiya, babban Limamin masallacin Juma’a na unguwar Zango, Malam Hassan Usman Zango ya bukaci iyaye da su sa ido sosai a kan ’ya’yansu, domin duk wanda ya yi sake game da tarbiyyar ’ya’yansa har suka lalace, to tabbas zai dandana kudarsa ranar gobe kiyama.
“Kuma muna fatar shiriya ga duk wata yarinya ko babbar mata da ta dauki karuwanci a matsayin hanyar samun kudi. Kuma ya kamata al’umma su fahimci cewa zina tana daya daga cikin abubuwan da ke haifar da talauci da yunwa da tsadar kayan abinci kuma duk kasar da ake yawan aikata zinace-zinace da shaye-shayen miyagun kwayoyi, zai yi wahala ’yan kasar su samu ci gaba da kwanciyar hankali.
“Saboda haka ya kamata hukumomi su dauki matakin da ya kamata a kan dukkan wuraren da ake zargi ana aikata badala da sauran miyagun laifuffuka. Wadanda suka samu kansu cikin wannan matsala, Allah Ya shirye su da sauran Musulmai baki daya.” Inji Limamin, a bayaninsa ga Aminiya.
Ya zuwa yanzu dai, kowane titi daga cikin manyan titunan cikin garin Bauchi, da zarar mutum ya tsaya da mota ko babur kirar roba-roba, tun daga karfe 6 na yamma har zuwa 10 na dare, sai ka samu ’yan mata suna jiran abokan hulda. Da zarar mutum ya tsaya da mota, za su fara gaishe shi, “barka da rana Alhaji.”

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited