Daurawa ya nemi iyaye su goyi bayan hukunta masu fyade
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Daurawa ya nemi iyaye su goyi bayan hukunta masu fyade

Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano Sheikh Ibrahim Aminu Daurawa ya bukaci iyaye su ba da goyon baya wajen hukunta masu yi wa yara fyade. 

Kwamandan ya yi kiran ne a yayin bikin Ranar ’Yancin dan Adam ta Duniya da aka gudanar a Kano.
Sheikh Daurawa wanda ya samu wakilcin Mataimakinsa Malam Idris Umar ya ce sau da yawa idan aka kama mutumin da ya yi fyade aka kuma gurfanar da shi gaban hukuma, sai iyayen yara su ki ba da hadin kai, “A karshe ma sai mu ji wai an yi sulhu a gida kuma abin takaicin shi ne a mafi yawan lokaci ma yafiya ake yi ga mai laifin,” inji shi.
Ya ce abin da iyayen suke yi shi zai sa wani ya je ya aikata irin wannan laifi, domin ya san ba abin da zai same shi na hukunci. Ya ce, “Sau da yawa sai an kama mai laifi an kawo shi, idan muka nemi iyayen yarinya sai ka ga suna nokewa, ta haka ne sai maganar ta balbalce.”
Kwamandan ya ce su a Hukumar Hisbah ba su barin laifin fyade ya mutu a gabansu ba sai sun kai gaban alkali in ya so a gaban alkalin iyayen su janye karar da kansu.
Da farko a jawabin Shugaban Gamayyar kungiyoyin Kare Hakkin dan Adam na kasa (Human Rights Network) da suka shirya taron Kwamared A.A. Haruna Ayagi, ya ce sun kafa wannan hadaka ce don tabbatar da ’yancin dan Adam a Najeriya. Ya nemi iyaye da jama’a su ba su goyon baya domin cimma muradinsu.
Taron ya samu halarta mutane daban-daban da suka hada da lauyoyi da Hukumar Yaki da Fataucin Mutane da Gallaza wa kananan Yara da ’yan sanda da kungiyoyi daban-daban daga Jihar Kano da kewaye.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited