An yi jana’izar dan sandan da aka kashe a Jihar Ribas
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

An yi jana’izar dan sandan da aka kashe a Jihar Ribas

A ranar Litinin da ta gabata ne aka yi jana’izar dan sandan nan da aka yi wa kisan gilla yayin gudanar da zaben cike- gurbi a Jihar Ribas a ranar Asabar da ta gabata.

dan sannda Sufurtanda Muhammad Alkali, mahaifinsa, wanda tsohon Kwamishinan ’Yan sanda Alhaji Yakubu Alkali da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Neja Alhaji Zubairu Mu’azu ne suka tarbi gawarsa lokacin da ta iso garin Minna da misalin karfe daya da rabi na ranar.
An yi jana’izarsa ne a garinsu da ke karamar Hukumar Bosso a Jihar Neja.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited