Makiyan Buhari ne ke haddasa tsadar abinci – Sarkin Borgu
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Makiyan Buhari ne ke haddasa tsadar abinci – Sarkin Borgu

Mai martaba Sarkin Borgu Alhaji Muhammadu Sani dantoro Kitoro na Hudu, ya ce wadansu batagari da suka wawashe asusun kasar nan su ne suka kitsa tashin farashin kayan abinci da kayan masarufi a kasuwanin kasar nan da gangan domin su shafa wa gwamnatin Shugaba Buhari kashin-kaji saboda yaki da cin hancin da take yi.

Alhaji Sani dantoro ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan nada Darakta Janar na kungiyar Cusa Kishin kasa a Zukatan ’Yan Najeriya, Ambasada Abubakar Tsanni a matsayin “Mabudin Borgu” a karshen makon jiya.
Sarkin ya ce wadanda suka barnatar da kudin kasar nan suna tura yaransu zuwa kasuwanni don saye kayan abinci kamar su shinkafa da wake da sauransu suna boyewa don haifar da tashin farashin kayan masarufi tare da wahalar da talakawan kasar nan.
“Mun san irin wahalar da muka sha a shekara 16 da suka gabata, inda wadansu suka sace kudin kasar nan suka boye a wurare da yawa,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa “Mutane suna saye kayan abinci don su kawo tashin farashin kayan masarufi. Suna amfani da kudin da suka sace daga asusun gwamnatin Najeriya. Suna boye kayan abinci don a samu matsanancin karancin abinci don mutane su wahala. Wannan rashin tausayi ne. Me suke son gwamnati ta yi a wannan hali?”
Ya ce lokacin da ya gano cewa hakan yana faruwa a masarautarsa sai ya dauki matakan da suka dace don kada mutanensa su sha wahala. “Mun ga yadda mutane suka rika fito da miliyoyi suna saye kayan abinci daga wurin mutanenmu suna fita da shi har ta kai farashin abinci ya yi tashin gwauron zabo. Sai na kira taro da jami’an tsaro da dagatai muka cimma matsaya cewa ba za mu sake barin wani ya fita da kayan abinci masu yawa ba daga yankunanmu. A da mudun shinkafa ’yar gida ana sayar da shi Naira 500 zuwa 600 amma daga lokacin da muka dauki matakin mudun ya sauko zuwa Naira 200 250,” inji shi.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited