karancin kudi ne matsalar jami’o’i - Farfesa Faborode
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

karancin kudi ne matsalar jami’o’i - Farfesa Faborode

Sakatare Janar na kungiyar Shugabannin Jami’o’i ta kasa, Farfesa Micheal O. Faborode ya ce karancin kudi ne babban kalubalen da ke fuskantar jami’o’in kasar nan.

Farfesa Faborode ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da wakilin Aminiya a Abuja a karshen makon jiya, inda ya ce dole ne gwamnati ta wadata jami’o’i da kudi muddin tana son a yi maganin kalubalen da ke addabar jami’o’in kasar nan. “Babu shakka kudi yana da matukar muhimmanci. Sannan kuma kashe kudin ta hanyar da ta dace shi ma yana da muhimmanci,”inji shi.
Ya ce babu yadda za a samu nasara har sai gwamnati ta fahimci cewa ilimi yana da muhimmanci kuma da gaske take ta bunkasa shi. Ya nuna takaici kan rashin alaka a tsakanin bangaren ilimi da bangaren tattalin arzikin kasar nan.
Ya ce babu shakka wannan matsala ce babba ga bangaren jami’o’in kasar nan tare da bunkasar ilimi, inda ya ce jami’o’i su ne suke rike da makomar kasar nan kamar yadda yake a wasu kasashe da suka ci gaba.
Farfesan ya kara da cewa sai kasar ta yi maganin matsalar da ke addabar manyan makarantunta sannan kasar za ta fita daga matsalar da ta samu kanta a ciki.
Ya bayyana cewa ci gaban da kungiyar ta samu sun hada da shirya taron kara wa juna sani ga mambobin kungiyar tare da hada kan jami’o’in kasar nan.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited