A kori Sakataren Gwamnatin Tarayya daga aiki - Majalisa
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

A kori Sakataren Gwamnatin Tarayya daga aiki - Majalisa

Majalisar Dattawa ta bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauke Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mista Babachir Dabid Lawal daga kan mukaminsa kuma a gurfanar da shi a gaban shari’a saboda saba ka’idojin aikin gwamnati.

Majalisar Dattawan ta dauki wannan mataki ne bayan ta karbi rahoton wucin-gadi na kwamitin da ta kafa a karkashin Sanata Shehu Sani na APC daga Kaduna domin binciken zargin karkatar da kudade da kuma kayan agaji da ake tura wa ’yan gudun hijirar Boko Haram (PINE).
Rahoton kwamitin dai ya zargi Sakataren Gwamnatin da kuma wani kamfaninsa da hannu a badakalar kwangilar da shirin na tallafawar ya bayar a karkashin kulawar Sakataren Gwamnatin.
Da yake mika rahoton Sanata Shehu Sani ya yi zargin cewa an yi keta dokar bayar dabkwangila ta shekarar 2007 domin yin zurmuke a cikin kwangilar. Ya ce: “An ba wa Kamfanin Babachir mai suna Rholabision Engineering Limited kwangilar bayar da shawara kan yadda za a cire ciyawa a sansanonin ’yan gudun hijira a Jihar Yobe a ranar 8 ga Maris din bana. Duk da cewa Babachir ya sauka daga mukamin darakta a kamfanin a watan Satumban bana, yana nan a cikin kundin bayanan kamfani cewa yana sanya hanu wajen shiga da fitar kudade a kamfanin.”
Ya ce kwamitin ya gano cewa an biya kashi 95 zuwa 100 na dukkan kwangilolin da shirin na PINE alhali wasu kwangilolin har yanzu ba a kammala su ba.
Sai dai a martanin da ya mayar ta hanyar sakon waya ga jaridar Aminiya a shekaranjiya Laraba, Mista Lawal ya ce akwai wani shiri na cin dunduniya da bata suna a cikin lamarin ta yadda yake ganin bai ma kamata ya damu kansa a kai ba.
Lawal ya ce, “Almundahama ne yake mayar da martani domin bata suna dukkan mutanen kirki. Da dama daga cikin masu kiran in sauka daga mukamina manyan abokan cinikin EFCC da ICPC da kotuna ne da har yanzu suke zama a kan kujerunsu na majalisar ba bisa ka’ida ba.
Ya kara da cewa,”Na ga rahoton da suka fitar, inda suka ce ban sauka daga mukamina na shugabancin kamfanin Rholabision Nigeria Limited. Amma ina son gaya muku cewa, na kafa kamfanin a watan Disamban 1990, kuma na sauka daga shugabancin kamfanin a watan Agustan 2015.”

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited