Ban yarda a kashe wani saboda xaukar fansa ba – Sarkin Jama’a
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Ban yarda a kashe wani saboda xaukar fansa ba – Sarkin Jama’a

Mai martaba Sarkin Jama’a Alhaji Muhammadu Isa Muhammad, ya ce bai lamunci wani da ke qarqashin masarautarsa ya kashe kowa da niyyar xaukar fansa kan kashe wani ba, maimakon haka a bar jami’an tsaro su riqa gudanar da bincike tare da xaukar matakin da ya dace.

Sarkin, wanda ya bayyana haka a fadarsa a ranar Litinin a lokacin da yake ganawa da masu unguwanni da dagatai da hakimansa kan yadda za a shawo kan tashe-tashen hankulan da ya ce suna neman fin qarfin ikonsu, ya ce idan sarakunan ba su yiwa tufkar hanci ba, lamarin na iya zama na qasa gaba xaya.
Sarkin ya bayyana cewa dukan rikice-rikicen da suke tasowa a Kudancin Kaduna babu wanda ya tava samo asali daga masarautarsa, sai dai waxansu marasa son zaman lafiya da ke qoqarin shigo da shi ta hanyar sanya shingaye a kan hanya suna tare mutane suna kashewa, inda ya nuna takaicinsa kan yadda xan Adam zai kama mutum xan uwansa ya yi masa yankan rago.
Da ya waiwayo kan masu riqe da rawunna, Sarkin ya gargaxe su cewa, “Na tara ku ne don in jawo hankalinku kada wani ya kuskura ya bar waxansu su kashe wani a yankinsa. Duk lokacin da aka ga wani na neman haifar da fitina idan ba za a iya magancewa ba a kai wa hukuma.”
Ya qara da cewa, “Duk Musulmi da Kiristan da ke qarqashin masarautata daidai suke a wajena bai kamata ku bar waxansu vatagari su zo su vata kyakkawar zamantakewar da ke tsakaninku daga waje ba. Ya kamata Musulmi su riqa tsare majami’un da ke yankinsu, su ma Kiristoci su riqa tsare masallatan da ke yankunansu.”
A lokacin da yake jawabi a wajen taron, Mataimakin Shugaban Gamayyar Coci-Cocin (Pentecostal Fellowship of Nigeria), reshen Jihar Kaduna kuma shugaban Cocin Goodnews Power Base da ke Layin Abuja a cikin garin Kafanchan, Fasto Emmanuel E. Baqo ya nuna farin cikinsa ne da damar da Sarkin ya ba shi tunda farko. “Ba zan tava mantawa da wannan ranar ba. Ka umurce ni in buxe taro da addu’a alhali ni kaxai ne Kirista a nan, haqiqa ka nuna kai uba ne ga kowa,” inji shi.
Faston ya bayyana cewa duk abubuwan da suka faru a baya rashin fahimtar juna ne ya janyo “Amma tun shekarar 2013 muka samu fahimtar juna da Mai martaba kuma tun sannan muke aiki tuquru wajen fahimtar da jama’armu cewa Sarkin Jama’a mutum ne mai son zaman lafiya da kowa. Cocina yana masarautarsa ce kuma ba ni da wani waje da ya wuce nan garin, asalina xan qabilar Koro ne daga garin Shadalafiya, amma ba abin da zan koma in yi a can, Kafanchan ne garina kuma a nan zan mutu,” inji shi.
Ya ce tun lokacin da suka samu fahimtar juna suke zaman lafiya a unguwarsu tsakanin Musulmi da Kirista a unguwarsu, “Ko yau ma Musulmin unguwarmu su suka tsare min cocina a Layin Abuja,” inji shi.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited