Gwamnatin Filato za ta kashe Naira biliyan 5 domin gina hanyoyi a birnin Jos
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Gwamnatin Filato za ta kashe Naira biliyan 5 domin gina hanyoyi a birnin Jos

Gwamnatin Jihar Filato za ta kashe kimanin Naira biliyan 5 wajen gina hanyoyi a cikin garin Jos da kewaye. 

Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar, Malam Muhammad Nazif ne ya bayyana haka a lokacin da yake miqa aikin xaya daga cikin hanyoyin ga kamfanin da zai gudanar da aikin. Ya ce gwamnatin jihar qarqashin jagorancin Gwamna Simon Lalong ta xauki qudirin ganin ta tallafa wa al’ummar jihar, ta hanyar samar musu da abubuwan more rayuwa.
Kwamishinan ya ce a lokacin da Gwamna Lalong ke yaqin neman zave ya gana da al’ummomin jihar, don haka ya san irin abubuwan da suke buqata.
Ya ce hanyoyin da gwamnatin za ta gina a cikin garin Jos da kewaye guda 8 ne, kuma kowace tana da tsawon kilomita 7. Ya ce hanyoyin sun haxa da hanyar Babbar Kasuwar Jos da hanyar Danserina-Pump da Hanyar Dutse Uku da Hanyar Baptist zuwa mahaxar makarantar St-Michael. Sauran su ne hanyar Tsohon ’Yarkasuwa da Rikkos Chwell-Nyap zuwa ’Yan tirela
Malam Nazif ya ce tun a makon jiya gwamnatin ta miqa aikin hanyoyin Unguwar Rogo da Tudun Wada -Kabong.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited