Makarantar Tazkiya ta yi bikin cika shekara xaya da kafuwa
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Makarantar Tazkiya ta yi bikin cika shekara xaya da kafuwa

Makarantun Tazkiya da ta haxa da sashen karatun boko da na Islamiyya da kuma haddar Alqur’ani da ke garin Kafanchan ta gudanar da bikin cika shekara xaya da fara karatu tare da zaven shugabannin kwamitin da zai riqa shirya irin wannan biki a kowacce shekara.

Bikin, wanda aka gudanar da shi a harabar makarantar da ke Layin Jama’a a garin Kafanchan, ya samu halartar iyayen yara maza da mata.
A jawabin xaya daga cikin shugabannin makarantar, Malama Rashida Umar Xanbaba ta ce makarantar ta fara ne da xaliban da ba su fi 10 ba, amma yanzu tana da xalibai 140. Malamar ta qara da cewa cikin nasarorin da makarantar ta samu ba ya ga ilimin boko da na addini da suke bayarwa, suna qarfafa wa yaran yin magana da harshen Ingilishi da Larabci.
A jawabin shugaban makarantar Malam Abdurra’uf Abdullahi, ya koka ne kan yadda ake samun qarancin biyan kuxin makaranta daga waxansu iyayen yara inda ya ce haka ba qaramin tsaiko ba ne ga qoqarin da malamai ke yi wajen bayar da ilimi ga yara waxanda su ne manyan gobe.
A jawabin da ya gabatar kan faxi-tashin da makarantar ta yi, Malam Shafi’i Jume ya ce wannan makaranta, kamar sauran makarantun Tazkiya da ke Najeriya, suna qarqaqashin kulawar babban limamin riqo na Masallacin Qasa da ke Abuja, Sheikh Ibrahim Maqari kuma cibiyarta a Zariya take sai dai tana da rassa a jihohi da garuruwan Arewa, kuma babban maqasudinta shi ne bayar da nagartaccen ilimin addini da na zamani tare da bayar da tarbiyya ga ’ya’yan Musulmi.
Ya bayyana irin qalubalen da Musulmi ke fuskanta a yankin ta yadda qarancin makarantun zamani da asibitoci na Musulmi kan sa iyaye tura ’ya’yansu makarantun mishan don kawai sun iya Ingilishi ba tare da la’akari da wace tarbiyya a ke cusa wa ’ya’yansu ba.
Shugaban Qungiyar Iyaye da Malamai ta makarantar, Alhaji Iro Ahmadu Xanmaiqosai, ya yaba qoqarin da malaman makarantar ke yi tare da aiki tuquru don ganin ’ya’yansu sun samu ilimi mai inganci.
An zavi Alhaji Dauda Xanlami a matsayin Shugaban Kwamitin yayin da Alhaji Musbahu Ado ya zama Sakatare. Sauran su ne Malam Jibril Badamasi, Sakataren Shirye-Shirye da Malam Rabi’u, Sakataren Watsa Labarai da Hajiya Ladi da Malam Ade Adedeoyin a matsayin Mai bayar da Shawara da kuma Jami’in Jin Daxi da Walwala.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited