Hukumar DSS ta kama Suswam da bindigogi
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Hukumar DSS ta kama Suswam da bindigogi

Hukumar Tsaron Qasa (DSS) ta bayyana qwato wasu bindigogi da takardun mallakar filaye 21 da sauransu baya ga motoci biyu a harabar wani kamfani mai suna, Dunes Investment and Global Properties Limited da ke Abuja.

Wata sanarwa da wani jami’in Hukumar DSS mai suna Tony Opuiyo ya raba wa manema labarai a Abuja a ranar Lahadin da ta gabata, ta yi zargin cewa takardun mallakar filayen da makaman da sauran kayayyakin da aka qwato mallakar tsohon Gwamnan Jihar Benuwai ne Mista Gabriel Suswam.
Mista Suswan, ya kai kansa ga Hukumar DSS bayan da ta gayyace shi a ranar inda har zuwa dare yake amsa tambayoyi.
Hukumar DSS ta ce ta yi amfani da takardar umarni kotu ne wajen bicikar kamfanin da yake lamba 44 a kan titin Aguiyi Ironsi Way, Maitama, Abuja, da misalin qarfe 9:00 na dare a ranar Asabar zuwa qarfe 2.42 na asubahin ranar Lahadi.
Hukumar DSS, ta samu jimillar harsasai 85. Kayayyakin da aka qwato sun haxa da wata bindiga qirar Glock haxe da maqunshin harsashi biyu da harsasai 29 da wata qirar Mini-Uzi da maqunshin harsashi biyu xauke da harsasai 10 da wasu harsasai huxu da kuma qarin harsasai 42 da wata qaramar bindiga mai sarrafa kanta da kuma bindiga qirar AK-47 a cikin motoci biyu da ke haabar kamfanin.
Sauran kayayyakin da aka gano a harabar sun haxa da wasu agogon qasaita guda 23 da kuma mabuxan motoci masu tsada guda 45.
Sanarwar t ace: “An gudanar da binciken ne sakamakon samun rahotannin sirri cewa akwai wau kayayyaki masu haxari a wuraren ajiye kaya na motocin da aka ajiye su a ginin, musamman motoci qirar Marsandi samfurin Mercedes Benz S550 (mai lamba BWR 135 AH) da Masarati 4.7 (mai lamba BWR 207 AJ), waxanda aka samu nasarar kama su.”
Hukumar DSS ta ce a gaban waxansu jami’an tsaro biyu da kamfanin Dunes Investment ya xauka aiki aka bincike motocin biyu da misalin qarfe 10:00 na dare a ranar Asabar xin.
Tsohon Gwamna Suswam yana fuskantar tuhuma kan almundahanar Naira biliyan 3 da miliyan 100, bayan da Hukumar Yaqi da yi wa Tattalin Arzikin Qasa ta gurfanar da shi da Kwamishinan Kuxinsa Omodachi Okolobia a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Maitama, Abuja a qarqashin Mai shari’a A.R. Muhammad kan zarge-zarge tara da suka haxa da haxin baki da cin hanci da rashawa da tozarta muqamansu a ranar 10 ga Nuwamban, shekarar 2015. Sai dai sun musanta zarge-zargen.
Hukumar DSS ta yi gargaxin cewa ba za ta lamunci duk wani aiki na keta doka daga mutanen da suka kamata a ce sun kasance masu bin doka da oda da sanin ya kamata ba.
Ta ce, “Ta lura da kalaman tunzurawa da waxansu ’yan siyasa ke yi domin zafafa harkokin siyasa a qasar nan.”
Hukumar DSS ta bayyana, “Damuwarta kan waxannan ’yan siyasa waxanda a qoqarinsu na neman magoya baya suka koma suna furta kalaman qiyayya har ma da xaukar nauyin kamfe a gidajen rediyo da talabijin alhali ba a buxe fagen irin wannan kamfe ba, kamar yadda dokar zave ta tanada.”
Hukumar ta soki wasu kafafen watsa labarai kan “Yadda suka tsoma kansu wajen rashin kishin qasa… ta hanyar tsunduma kansu cikin wannan mugun abu na rarraba kan jama’a wanda ya sava wa dokokin aikinsu na kasancewa fallen a huxu na gwamnati.”
Hukumar tsaron ta ce: “Za ta san qafar wando xaya da duk wanda yake yin duk wani aiki da ka iya jawo tashin hankali a qasar nan komai matsayinsa.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited