Ana qarin gishiri kan rikicin Kudancin Kaduna – Kwamishinan ‘yan sanda
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Ana qarin gishiri kan rikicin Kudancin Kaduna – Kwamishinan ‘yan sanda

Daga hagu Kwamandan Runduna taKwamishinan ’Yan sandan Jihar Kaduna, Mista Agyole Abeh ya ce ana qarin gishiri a kan adadin mutanen da aka kashe ko gidajen da aka qona a rikicin da ke faruwa a Kudancin Kaduna, don cimma wata manufa ta son kai.

Kwamishinan ya bayyana haka ne bayan zagayawa da wakilan kafafen watsa labarai yankunan Goska da Dangoma da Bakin Kogi da ke Qaramar Hukuma Jama’a. Ya ce: “Ana samun hare-hare tsakanin masu faxa da juna lokaci bayan lokaci. Wasu hare-haren ba a bayyana su ko kawo rahotanninsu sai bayan an kai harin ramuwa ko xaukar fansa. Duk lokacin da aka ci gaba da kai hare-hare dole ne a riqa samun harin xaukar fansa.”
Kwamishinan ya shaida wa mutanen yankin cewa aikin kawo zaman lafiya ya kawo su yankin kuma babu ruwansu da qabila ko addinin mutum domin Gwamnatin Tarayya ce ke biyansu ba wani ba, don haka za su yi aiki tuquru don samar da zaman lafiya a yankin.
A jawabin, Kwamandan Runduna ta Xaya da ke Kaduna, Birgediya Janar Isma’il Isa, ya ce waxansu na zarginsu da rashin kawo xauki da wuri idan wani abu ya faru inda ya ce, “Dukan vangarorin da ke faxa da juna kowanne na da laifi. Waxansu na zargin rashin isowarmu da wuri idan ana rikici. Mu masu rabon faxa ne ba ma goyon bayan kowa. Sakamakon amsa kiran da muka yi ne ya sa mutanenmu suka kashe mutum biyu daga cikin masu kawo hari yayin da su kuma maharan suka kashe xan sanda xaya, aikinmu shi ne samar da zaman lafiya da kiyaye aukuwar tarzoma.”
Kewayen, wanda ya qunshi shugabannin tsaro na yankin, ya biyo bayan dawowa da harkokin tsaro ne zuwa yankin da Kwamishinan da Kwamandan suka yi don samar da zaman lafiya na dindindin.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited