Tun ana biyan Naira 500 kuxin kujera nake zuwa aikin Hajji - Laraba Harisu
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Tun ana biyan Naira 500 kuxin kujera nake zuwa aikin Hajji - Laraba Harisu

n Hajiya Laraba Harisu Gadar GayanWata dattijuwa mai suna Hajiya Laraba Harisu Gadar Gayan da ke Qaramar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna ta ce, tun a zamanin da ake biyan Naira 500 a matsayin kuxin kujera take zuwa aikin Hajji a qasar Saudiyya. 

Hajiya Laraba Harisu ta ce a bana idan Allah Ya yarda aikin hajjinta na 32 ke nan kuma duk biya take yi da kuxinta.
Hajiya Laraba ta bayyana haka ne a zantawarta da Aminiya a wajen bitar da ake yi a duk mako ga maniyyatan Jihar Kaduna a garin Rigachikun.
A cewarta aikin Hajji a shekarun baya da yadda ake yi a yanzu akwai bambanci sosai. “Qwarai ina cikin waxanda da ke da niyyar zuwa aikin Hajji a bana da yardar Allah. Kuma duk ranar bita da ni ake farawa a kuma naxe da ni. Abin da kawai zan ce shi ne masu niyyar zuwa aikin Hajji su xaure su riqa halartar bita domin koyon yadda ake gudanar da aikin,” inji ta.
Ta qara da cewa: “Idan suna zuwa bitar za su qaru da abubuwan da za su taimaka musu wajen inganta aikin hajjinsu. Bana idan Allah Ya yarda ina da Arafa 32 kuma duk shekara sai na halarci bita domin koyan yadda ake gudanar da aikin Hajji. Don haka wanda ba ya zuwa ya yi qoqari ya riqa zuwa domin zai qaru da abubuwa da yawa.”
Hajiya Laraba ta ce: “Kuma a tsawon shekarun nan da na yi ina aikin Hajjin nan duk biya nake yi da kuxina ban kuma tava samun kujerar gwamnatin ba kamar yadda nake ji waxansu na yabawa. Tun ana biyan Naira dubu xaya make zuwa aikin hajji kai na je aikin Hajjin a lokacin ana biyan Naira xari biyar kuxin kujera.
A zamanin ba a ba ki jaka, ba a baki riga duk da kuxinki za ki saya. Kuma insha Allahu mun je lafiya mun kuma dawo lafiya. Har yanzu kuma ba a tava zargi ko samunmu da aikata laifi ba a qasar Saudiyya.”

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited