Jibi Sarkin Musulmi zai jagoranci yi wa Shugaba Buhari addu’a a Kaduna
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Jibi Sarkin Musulmi zai jagoranci yi wa Shugaba Buhari addu’a a Kaduna

Jibi lahadi idan Allah Ya kai mu Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar zai jagoranci malaman Musulunci wajen yi wa Shugaban Qasa Muhammadu Buhari da qasar nan addu’o’in samun lafiya da zaman lafiya a garin Kaduna.

Babban Sakataren Jama’atu Dokta Khalid Abubakar Aliyu ya shaida wa manema labarai cewa an shirya gudanar da addu’o’in ne da haxin gwiwar Jama’atu da Majalisar Malamai ta jihar bisa umurnin Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar.
Ya ce qasar nan tana bukatar addu’a ta musamman domin neman taimakon Allah Ya yaye mata matsalolin da suke damunta, musamman matsalolin karyar tattalin arziki da rikicin Kudancin Kaduna da rashin lafiyar Shugaba Muhammadu Buhari.
Babban Sakataren ya ce ana sa ran Sarkin Musulmi da Gwamnan Jihar Nasir El-Rufa’i da Sarkin Zazzau da Sarkin Jema’a da manyan malaman addinin Musulunci, za su halarci addu’o’in. “Batun rashin lafiyar Shugaba Buhari na xaya daga cikin matsalolin da ke damun qasar nan. Hakan ya sa bisa umarnin Sarkin Musulmi Jama’atu Nasril Islam da haxin gwiwar Majalisar Malamai ta Jihar Kaduna suka shirya taron addu’ar roqa masa lafiya. Haka batun rikicin Kudancin Kaduna da ye neman zama wutar daji shi ma za mu roqi Allah Ya kawo mana qarshensa da sauran matsalolin da suke damun qasar nan. Kuma za a yi taron ne a ranar Lahadi (jibi,” inji shi.
Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Sheikh Usman Babantune ya ce suna da hujjoji a shari’ance da suke nuna cewa wannan mataki bai sava wa Musulunci ba. Sheikh Babantune ya yi addu’ar Allah Ya dawo da Shugaba Buhari lafiya ya koma bakin aikinsa lafiya.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited