Jihar Adamawa ta ba da kwangilar gina gada
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Jihar Adamawa ta ba da kwangilar gina gada

Gwamna Mohammed Jibrilla Bindow na Jihar AdamawaGwamnan Jihar Adamawa Alhaji Muhammadu Jibrilla Bindow ya ba da kwangilar gina gada a Qaramar Hukumar Song wadda ta fi shekara 60.

Gadar wadda aka yi ta tun lokacin Turawan mulkin mallaka kafin a samu ’yancin kai, bayan samun ’yancin kai gwamnatoci da dama sun yi alqawarin gina ta amma ba su gina ba.
Gwamna Jibrilla Bindow ya ba da kwangilar ne ga Kamfanin Triacta a kan naira miliyan 585 wanda ya yi alqawarin kammala aikin a cikin wata huxu.
Gwamna Bindow ya ce kwangilar gina gadar ya bayar da ita ce domin cika alqawarin da ya xauka a lokacin da yake kamfe. “Allah Ya kawo mu lokaci a yau na ba da kwangilar gadar mai tarihi wadda Turawan mulkin mallaka na Jamus suka yi,” inji shi.
Kwamishinan Ayyuka ta Jihar Misis Lilian Stephen ta jinjina wa Gwamnan kan cika alqawarin da ya xauka da kuma sake sanyawa a gina gadar mai tarihi da gwamnatoci da dama suka share a qalla yau shekara 50 ke nan a jihar.
Wakilin Diraktan Kamfanin Triacta, Injiniya Imran Amin ya ce za su kammala gadar a daidai lokacin da aka ba su.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited