Za a hana maniyyatan da ba su halartar bita zuwa aikin Hajji – Namadi Musa
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Za a hana maniyyatan da ba su halartar bita zuwa aikin Hajji – Namadi Musa

Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar KadunaBabban Daraktan Mai Kula da Ma’aikatar Addinai ta Jihar Kaduna, Injiniya Namadi Musa ya ce jihar na gab da hukunta maniyyata da ba su halartar bita domin koyon yadda ake gudanar da aikin Hajji ta hanyar cire sunayensu daga cikin masu zuwa sauke farali a bana.
Alhaji Namadi Musa ya ce, abin bakin ciki ne yadda maniyyata za su biya kuxi masu yawa domin zuwa sauke farali, ba tare da sanin farillai da sunnoni ko mustahaban aikin Hajjin ba.
Ya ce ba a bautar Allah da jahilci, saboda haka akwai buqatar duk maniyyaci ya nemi ilimin yadda ake aikin Hajji kafin ya tafi Qasa Mai tsarki.
“Gaskiya muna gab da hana maniyyata marasa halartar bita zuwa aikin Hajji daga Jihar Kaduna zuwa aikin, domin bitar nan tana da matuqar muhinmanci. Kuma ba mu jin daxin ganin maniyyata sun biya kuxi sama da Naira miliyan xaya amma a ce sun je Makkah ba su san yadda ake gudanar da aikin Hajji ba.
Kuma ga shi malamai suna ta faxin cewa ba a bautar Allah da jahilci. Saboda haka ina kira ga maniyyata su daure su riqa halartar wannan bita da muke shirya masu domin samun damar yin aikin Hajji karvavve,” inji shi.
Babban Daraktan wanda shi ne Mai Bai wa Gwamnan Jihar Shawara Kan Al’amuran Addini da Aikin Hajji, ya bayyana haka ne a ranar Asabar da ta gabata, lokacin da ya ziyarci wuraren da ake gudanar da bita ga qananan hukumomi da ke Kinkinau a Qaramar Hukumar Kaduna ta Kudu da na Kwalejin Sardauna a Qaramar Hukumar Kaduna ta Arewa da kuma Sansanin Alhazai a Qaramar Hukumar Igabi.
Injiniya Namadi ya yaba kan da yadda ya ga malamai ke ilmantar da maniyyatan a wuraren da ya ziyarta.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited