’Yan sanda sun kama matasa bakwai kan lalata da qananan yara a Jigawa
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

’Yan sanda sun kama matasa bakwai kan lalata da qananan yara a Jigawa

Sufeto-Janar Idris K. Ibrahim’Yan sanda a Qaramar Hukumar ’Yankwashi da ke Masarautar Kazaure a Jihar Jigawa sun kama waxansu matasa bakwai da ake tuhumarsu da laifin yin lalata da qananan yara mata biyu a qauyen Sada da ke qaramar hukumar. 

’Yan sandan sun ce sun kama matasan ne a cikin wani kango inda suke lalata da qananan yaran a daidai lokacin da suke lalata da yaran (an sakaye sunansu), dukansu masu shekara 13 a duniya Wakilimmu ya samu labarin cewa matasan sun jima suna aikata wannan varna da qananan yara a qauyen amma aka gaza sanar da hukuma domin xaukar mataki sai a wannan karo ne dubunsu ta cika, bayan da wani mazaunin qauyen ya shaida wa ’yan sanda abin da suke yi.
Majiyarmu ta ce sakamakon haka ne aka xana wa matasan tarko aka sanar da ’yan sanda a daidai lokacin da aka ga shigar yara mata biyu cikin kangon, inda ’yan sandan suka kama matasan sun kafa layi suna yin lalata da yaran.
Waxanda aka kama sun haxa da Sirajo Ali da Sule Dare da Mani Xanladi da Hassan Mati da Abdu Xantsoho da Amadu Nanini.
Shugaban Qaramar Hukumar ’Yankwashi wanda ke gida Aujara a Qaramar Hukumar Jahun, ya shaida wa wakilinmu ta waya cewa yana gida ne saboda yana fama da ciwon kai mai tsanani a ranar, amma yana da labarin faruwa lamarin, ya ce waxanda ake zargin suna hannun jami’an tsaro.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa SP Audu Jinjiri ya ce suna da labarin faruwar lamarin amma ba ya gari ya yi tafiya. Ya ce abin da ya sani an kama matasan bakwai kuma suna hannun jami’an tsaro masu binciken manyan laifuffuka ana gudanar da bincike a kansu.
Ya ce da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da matasan bakwai a gaban alqali domin su fuskanci hukunci a kan laifin da ake tuhumarsu.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited