Dan Pele zai kwashe shekaru 13 a gidan yari
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Dan Pele zai kwashe shekaru 13 a gidan yari

Edinho a hagu da mahaifinsa PeleEdinho, dan shahararren dan kwallon kafa na duniya Pele wata kotu da ke Brazil ta yanke masa hukuncin daurin shekara 13 a gidan yari bayan ta same shi da laifin yin mu’amala da kwayoyin sa maye da kuma safarar kudi ba bisa ka’ida ba.

A shekarar 2005 ne jami’an tsaro suka yi ram da Edinho tare da wadansu abokan huldarsa a wata maboya da suke amfani da ita wajen yin hulda da miyagun kwayoyi da kuma safarar kudi ba bisa ka’ida ba a kasar Brazil.
Tun bayan da aka kama Edinho a shekarar 2015 ne ake shari’arsa a kotuna daban-daban amma sai a ranar Alhamis din da ta wuce ne wata kotu ta zartar masa da hukuncin daurin shekara 12 da watanni 10 a gidan kaso inda alkalin ya rage masa hukuncin daurin shekara 32 da wata kotu ta zartar a kan Edinho tun farko zuwa shekara 12 da watanni 10.
Shi dai Edinho, ya taba buga wa kulob din Santos na Brazil kwallo ne, kuma shi ne mai tsaron gida (gola) kafin ya yi ritaya. Mahaifinsa Pele ma a kulob din ya yi kwallo kafin ya yi ritaya.
Dan kimanin shekara 46 da haihuwa, Edinho yana daga cikin ’ya’yan Pele bakwai kuma da alama shi ne hatsabibi daga cikinsu, saboda yadda yake hulda da miyagun kwayoyi da safarar kudi ba bisa ka’ida ba. Sai dai Edinho ya ce zai daukaka kara don ya kalubalanci hukuncin da aka zartar a kansa. Ya ce a iya saninsa, bai yarda da laifuffukan da ake tuhumarsa ba.
Rahotanni sun nuna an sha iza keyar Edinho gidan yari a baya a lokuta daban-daban saboda laififfukan da yake aikatawa amma wannan shi ne hukunci mafi muni da wata kotu ta taba zartarwa a kansa.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited