Kotu ta tsare matashi da mahaifiyarsa kan yi wa yarinya cikiKotu ta tsare matashi da mahaifiyarsa kan yi wa yarinya ciki
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Kotu ta tsare matashi da mahaifiyarsa kan yi wa yarinya cikiKotu ta tsare matashi da mahaifiyarsa kan yi wa yarinya ciki

Wata Kotun Majistare da ke Bwari a yankin Birnin Tarayya, Abuja ta ba da umarnin a tsare wani matashi mai suna Japheth Adam tare da mahaifiyarsa kan zargin yi wa wata yarinya mai shekara 16 ciki.
Ana zargin matashin da yi wa yariyar ciki ne, yayin da mahaifiyarsa mai suna Mercy Adams aka zarge ta da yi wa yarinyar barazanar fuskantar matsala tare da abin da za ta haifa matukar ba ta zubar da cikin ba.
Mahaifin yainyar (an sakaya sunansa) wanda ya shigar da karar a kotun, ya shaida wa kotun a ranar Larabar makon jiya cewa, lamarin ya tilasta ’yarsa janyewa daga zuwa makaranta tare da fuskantar zirga-zirgar zuwa asibiti saboda matsalolin rashin lafiya da ta rika fuskanta bayan barazanar da matar ta yi mata.
Mahaifin ya shaida wa kotun cewa bayan da mahaifiyar yarinyar ta kula da alamun ciki tare da yarinyar, ta tuhume ta kan lamarin daga bisani aka tabbatar da hakan a wani asibiti bayan an yi mata gwaji.
Ya ce ’yarsu ta gaya musu cewa saurayin wanda makwabcinsu ne a kauyen Kado-Kuchi da ke Abuja ya yaudare ta ce ya rika yin lalata da ita a lokutan da mahaifiyarsa ta tafi aiki inda suka rika haduwa a dakin mahaifiyar wanda ake zargin a lokuta daban-daban.
A cewarsa bayan sun tuntubi wanda ake zargi a kan lamarin, ya amsa aikata laifin tare da amincewa da cikin a matsayin nasa. Sai dai ya shaida wa kotun cewa mahaifiyar yaron ta nuna bacin ranta da matsayar danta, sannan ta bukaci yarinyar ta zubar da cikin tare da barazanar fuskantar fitina matukar ba ta zubar ba.
Da alkalin kotun Mai shari’a Abdullahi Ahmad Ilelah ya juya gare shi, wanda ake zargin ya amince da aikata laifin tare da amincewa da cewa cikin nasa ne.
A nata bangaren, mahaifiyar yaron ta musanta zargin yin barazana ga yarinyar. Daga nan ne kuma lauyan wadanda ake zargin ya bukaci kotun ta ba da belensu.
Sai dai alkalin ya yi watsi da bukatar inda ya bukaci lauyan ya mika bukatar a rubuce don duba yiwuwar hakan. Alkalin ya kuma dage ci gaban shari’ar zuwa ranar 13 ga wannan wata.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited