Miji da ’yar uwarsa sun gurfana gaban kotu kan kashe matarsa
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Miji da ’yar uwarsa sun gurfana gaban kotu kan kashe matarsa

An gurfanar da wadansu ’yan uwan juna biyu a gaban Babbar Kotun Majistare ta 31 da ke Gyadi-Gyadi a birnin Kano, bisa zarginsu da hadin baki tare da kashe wata matar aure.
Tun farko dan uwan marigayiyar ce mai suna Hassan Sallau da ke Unguwar Gama ya kai rahoto ga ofishin ’yan sanda na Gwagwarwa cewa mutanen da ake zargin da kashe marigayiya Ladi Ishaya da suka hada da mijinta Ishaya Kantiyuk da ’yar uwarsa Hajarat Yakubu sun hada baki ne suka yi wa marigayiyar dukan kawo wuka lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarta.
dan sanda mai gabatar da kara Saje Saleh Nakawu ya shaida wa kotun cewa lamarin ya faru ne sakamakon fada a tsakanin marigayiya Ladi da ’yar uwar mijinta Hajarat Yakubu, inda mijin marigayiyar Ishaya ya rike marigayiyar lamarin da ya ba wa Hajara damar yi wa marigayiyar dukan kawo wuka har ta sume aka kai ta Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano inda likitoci suka tabbatar da mutuwarta.
Sai dai wadanda ake zargin sun musanta laifin, laifin da dan sanda mai gabatar da kara ya ce ya saba wa sashe na 221 da 97 na kundin laifuffuka da hukuncinsu na Final Kod.
Alkalin Kotun Mai shari’a Binta Ibrahim Galadanci ta bayar da umarnin a tsare wadanda ake zargi a gidan kurkuku tare da dage shari’ar zuwa ranar 28 ga watan Maris 2017 don ci gaba da saurarenta.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited