Hisba ta kama mashaya a Jigawa
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Hisba ta kama mashaya a Jigawa

Hukumar Hisba ta gurfanar da mata uku da maza uku a gaban Babbar Kotun Majistare ta Dutse a karkashin Mai shari’a Amina dahiru babura sakamakon kama su a wani otel da ake kira Dogo suna shaye-shaye.
Hukumar Hisbar ta kuma ce ta kama giya ta kimanin Naira miliyan daya da kayan kallo da kujeru da tebura a matsayin shaida.
Ita dai wannan shari’a ta gidan giya na Dogo shari’a ce da ta jima ana jan ta ba ta kare ba kusan shekara daya.
Mai shari’a Amina dahiru ta bukaci a gabatar mata da shaidun da ’yan Hisba suka kama a gidan amma saboda wasu kayan suna wata Kotun Majistare inda aka fara shari’ar da farko ba a gabatar da su ba a gabanta.
dan sanda mai gabatar da kara a gaban kotun, Muhammed Umar ya bukaci kotun ta dage sauraren karar zuwa ranar 14/3/2017 domin ba shi damar gabatar da shaidunsa.
Sai dai lauyan wadanda ake tuhuma, Omwun Kawome ya ce rashin gabatar da shaida a gaban kotun tamkar jan kafa ne domin a samu tsaiko a shari’ar, don haka ya bukaci kotu ta sa ’yan sanda su gabatar da shaidarsu a gabanta a ranar da kotun za ta sake zama.
Kotun ta sake dage sauraren karar zuwa ranar 14/3/17 kamar yadda dan sanda mai gabatar da karar ya nema. A wani labari an gurfanar da wadansu mutum biyar a gaban Babbar Kotun Majistare ta Dutse a karkashin Mai shari’a Amina dahiru babura ke jagoranci bisa zarginsu da kashe wasni mutum kan zarginsa da maita. Mutanen da suka fito daga karamar Hukumar Kiyawa, ana zarginsu ne da hallaka wani mutum da ke kauyen Bulori saboda zargin maye ne kuma shi ne ya cinye musu dan uwansu mai suna dalha Magaji.
dan uwan wadanda ake zargi mayen ne ya cince shi mai suna Malam Amadu Mati Bulliru, ya ce marigayin mayen ne ya cinye musu dan uwansu dalha Magaji, saboda kafin rasuwar Magajin ya yi ta ambatar sunansa yana cewa ga wane nan zai yanka ni, da sunansa ya mutu har ya cika wannan ne ya sa muka dauki doka a hannunmu muka je har gidansa muka auka masa ni da matan nan ’yan uwana da ka gani mun tsaya a gaban kotu.
dan sanda mai gabatar da kara a gaban kotun Muhammed Umar ya bukaci kotun ta dage sauraren karar domin ’yan sanda su samu damar nazari da bincike a kan lamarin.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited