Gwamnatin Kaduna ta haramta bara da talla a tiituna
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Gwamnatin Kaduna ta haramta bara da talla a tiituna

Gwamnatin Jihar Kaduna ta haramta talla da bara da kuma acaba a kan tituna a sakamakon wani  rahoton sirri da gwamnatin ta ce ta samu.
A cewar gwamnatin wannan daukar mataki ya zama wajibi saboda bayanan sirri da ta samu da ke cewa idan ba a dauki mataki ba komai na iya faruwa.
Kakakin Gwamnan Jihar, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka bayan kammala taron Majalisar Tsaro na mako-mako da ake yi a gidan gwamnati.
Mista Aruwan ya ce gwamnati ta umarci jami’an tsaro su fara aikin tabbatar da cewa kowa ya bi dokar sau da kafa. “Majalisar Tsaro ta Jihar Kaduna ta yanke shawarar haramta yin bara da talla a gefen titi tare da haramta yin acaba a cikin Jihar Kaduna. Wannan mataki an dauke shi ne da kyakkyawan nufi ba domin cin zarafin kowa ba. Manufarmu a gwamnati ita ce kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Saboda haka an umarci jami’an tsaro su tabbatar da cewa jama’a sun bi wannan doka sau da kafa. Muna fatan jama’a za su ba mu goyon baya ta yadda za a samu nasarar kare rayuka da dukiyoyinsu a jihar baki daya,” inji shi.
A wani labarin, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kaduna, Mista Agyele Abeh ya ce jami’an tsaro da suka hada da sojoji da ’yan sanda da sauransu sun yi nasarar maido da zaman lafiya a Kudancin Kaduna.
Ya ce tunda aka umarci su shi da Kwamandan Runduna ta daya, Birgediya Sama’ila Isa su koma Kudancin Jihar da zama, sun kama wadanda suke da hannu wajen tada fitina a yankin. “Muna murnar sanar da ku cewa mun yi nasarar rage hararen da ke faruwa a Kudancin Kaduna. Tunda muka koma yankin domin tabbatar da zaman lafiya muna ta aiki tare da sojin sama da na kasa a yankin,” inji shi.
Birgediya Sama’ila Isa ya ce rundunarsu za ta fara yin atisaye mai suna Harbin Kunama na Biyu a yankin domin tabbatar da tsaro.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited