Mutum 28 sun shiga hannu kan aikata miyagun laifuffuka a Jigawa
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Mutum 28 sun shiga hannu kan aikata miyagun laifuffuka a Jigawa

Rundunar ’Yan sanda Jihar Jigawa ta baje kolin wadanda take zargin barayin motoci ne da ’yan fashi da masu yi wa kananan yara fyade da yawansu ya kai mutum 28.
daya daga cikin wadanda ake zargi da fashi da makami a kan hanyar Gumel, mai suna Yakubu Alhaji Idris ya shaida wa wakilinmu cewa su takwas ne suka tare hanyar Maigatari zuwa Gumel kuma su biyu ne aka kama yayin da sauran abokansu suka tsere, kuma a cikinsu mutum daya kawai ya sani mai suna Ahmadu wanda shi ne ya jawo su.
Ya ce Ahmadu mazaunin Gunduwawa ne a Jihar Kano, yayin da sauran bai san daga inda suke ba, sai dai ya san daga Kano suke zuwa suke yin fashi, amma shi wannan ne karon farko da ya taba yin fashi da makami.
Shi kuwa Umar Abubakar da ake zargi da satar motoci a garin Kazaure da kewaye ya ce su ne suke dauke motocin jama’a suna kaiwa bukur a Jihar Filato suna sayar wa dillalai. Umar mai shekara 17, ya ce motoci uku ya sata ya kai Jihar Filato da suka hada da Fijo da Honda biyu.
Ya ce yana shaida wa dillalin motocin a Filato cewa babansa Kwastam ne kuma shi ne yake tura shi ya kai motocin ya sayar. Ya ce saboda haka ne dillalin motocin ya amince da shi yake sayen motocin a wajensa, sai a wannan karo da ya kai mota ta uku ne asiri ya tono aka kama shi.
Kama shi ya jawo kama mutum takwas da ake tuhuma da laifin sayen kayan sata da suka hada da dillalai da wani jami’in tsaro da ya sayi daya daga cikin motocin.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai, dillalin mai suna Umar bukur ya ce ba su san cewa yaron barawo ba ne domin ya nuna masu cewa mahaifinsa Kwanturola ne na Hukumar Kwastam a Jihar Jigawa kuma shi ne yake ba shi motocin yake kawowa a sayar masa.
Kwamashinan ’Yan sandan Jihar Jigawa, Rasheed O. Akintunde ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce za a gabatar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar sun kammala bincike.
A wani labarin kuma ’yan sanda sun kama wani magidanci mai suna Nura Garba bisa zarginsa da yi wa wata budurwa ’yar shekara 15 ciki a garin Birnin Kudu da ke Jihar Jigawa.
 Nura Garba mai kimamin shekara 50 da ke zaune a Unguwar Zarenawa, ya shaida wa ’yan sandan cewa shi ya yi yarinyar wadda aka sakayae sunanta ciki.
Ya shaida wa manema labarai cewa ya ba ta maganin zubar da ciki inda ta sha cikin da bai fi wata biyar ba ya zube dan ya fito ba rai.
Ya ce bayan da aka tsinci jaririn a wani kango da yarinyar ta jefar bincike ya sa aka kama ta ita kuma ta tona masa asiri ’yan sanda suka kama shi.
 Ya ce ya fara lalata da yarinyar ce kimanin wata biyar da suka gabata a wani kango dab da inda yake nikan inji, inda yake ba ta Naira 200 a duk lokacin da ya yi lalata da ita.
ne kachal bawani kudin kirki yake bataba Ya ce zai auri yarinyar da zarar iyayanta sun amince, kuma ya ce sharrin Shaidan ne ya ja shi ga aikata hakan.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited