Jami’o’inmu na bukatar karin kudi – Saraki
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Jami’o’inmu na bukatar karin kudi – Saraki

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Abubakar Bukola Saraki ya ce jami’o’in kasar nan na bukatar karin kudi don su yi gogayya da takwarorinsu na duniya.
Sanata Bukola Saraki ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a wurin taron kara wa juna sani da kungiyar shugabannin jami’o’i suka shirya a Abuja, a Larabar makon jiya.
Sanata Saraki wanda Shugaban Kwamitin Kula da Manyan Makarantu da Asusun Tallafa wa Manyan Makarantu (TETFUND) na Majalisar Dattawa Sanata Barau Jibrin ya wakilta, ya ce karin kudin zai taimaka wa jami’o’in kwarai da gaske. “Duk da matsalar tattalin arzikin da ake ciki a yanzu, jami’o’inmu suna bukatar karin kudi domin su yi gogayya da sauran jami’o’in duniya a fagen ilimi,” inji shi.
Ya ce hakan zai kara zaburar da masu ruwa-da-tsaki wajen kirkirowa da bullo da sababbin fasaha a jami’o’in.
Shugaban ya bayyana cewa Majalisar Dattawa ta himmatu wajen samar da yanayi mai kyau ga matasan kasar nan ta hanyar yin dokokin da za su taimaka ga jami’o’in.
Sanata Saraki ya nuna alhininsa kan yadda jami’o’i a yanzu suka koma, inda ya yi kira ga masu ruwa-da- tsaki su dauki matakan da suka kamata domin maganin matsalolin da suke addabar jami’o’in kasar nan.
Ya ce a shekarun 1960 zuwa karshen 1970, an san jami’o’in kasar nan da kwarewa a wasu fannoni.
Amma a cewarsa a yanzu jami’o’in na yin rige-rigen gudanar da wasu kwasa-kwasai wadanda ba su da kwarewa a kansu.
Ya ce hakan ke sanya a samu daliban da ba su da wata kwarewa. Daga nan sai ya shawarci jami’o’in su yi wa manhajojinsu da tsarin koyarwarsu garambawul domin samar da dalibai ingantattu.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited