Duk dan kwangilar da ya bar wurin aikinsa ku sanar da gwamnati – Gwamna Tambuwal
Saturday 24 June 2017     29 Ramadan 1438

Aminiya

A+ A A-

Duk dan kwangilar da ya bar wurin aikinsa ku sanar da gwamnati – Gwamna Tambuwal

Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya yi kira ga mutanen jihar musamman wadanda ke kananan hukumomin su kai rahoton duk dan kwangilar da aka bai wa aiki a kauyukansu, amma ya gudu ko yake yi wa aikin rikon sakainar kashi domin daukar matakin da ya dace.
Kakakin Gwamnan, Imam Imam ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa, inda ya ce Gwamnan ya yi wadannan kalamai ne a lokacin da ya yi taro da shugabannin kananan hukumomin jihar 23.
“Duk ayyukkan da ake yi muna yin su ne don amfanin jama’a kai-tsaye domin ba wata hujja da mutane za su rika yin biris da abubuwan da aka samar musu, ya kamata su sani fa nasu ne da yakamata su kare daga barnatawa da lalatawa duk wani aiki da ya samu inganci da kula bai kamata su bari ya shiga mawuyacin hali ba,” inji Gwamna Tambuwal.
Gwamna Tambuwal ya kara da cewa gwamnati za ta kara fito da wasu ayyuka a fannin lafiya da aikin gona da ilimi don cimma bukatun jama’ar jihar.
Ya yi kira ga shugabanin kananan hukumomin su fito da wasu hanyoyin samun kudin shiga a yankunansu domin ganin an samu kubuta daga halin rashin kudi da kasar ke fama da shi. “Akwai bukatar zage dantse wajen ganin an samar da kudin shiga a jiha da kananan hukumomi,” inji shi.
Game da umarnin sanar da gwamnati idan dan kwangila ya bar wurin aikinsa Malam Anas Buhari da ke kasuwanci a kan Titin Katsina a Sakkawato, ya shaida wa Aminiya cewa: “Na ji dadin kalaman Gwamna kan haka ne nake son mika kukana gre shi cewa a nan cikin gari, Titin Katsina da Titin Ibrahim Dasuki da Mabera Madan Karo da Katin Daji zuwa Gidan Dare da Gwiwa duk an kankare hanyoyin sama da wata uku amma ’yan kwangila sun bar wurin. Mu mutanen gari muna shan kura da wahala duk lokacin da muka bi hanyar, don haka ina sanar da Mai girma Gwamna ya dauki matakin don kammala hanyoyi da gine-gine da ya gada ga tsohuwar gwamnati wadanda aka daina aiki a kansu.”

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited