Gwamnatin Jigawa za ta gina gidan yari
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Gwamnatin Jigawa za ta gina gidan yari

Gwamnatin Jihar Jigawa ta sha alwashin gina kurkuku mai cin gado 300 a Dutse fadar jihar saboda wanda yake garin an gina shi ne tun zamanin Turawan mulkin mallaka a 1936 da nufin tsare mutum 50 amma ake tsare mutum 200 a halin yanzu.
Gwamnan Jihar Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar ya ce za a gina kurkukun ne da nufin kawo karshen cinkoso a kurkukun na Dutse.
Gwamna Badaru ya fadi haka ne lokacin da ya karbi bakuncin sabon Kwanturolan Gidan Yari na Jihar, Alhaji Magaji Ahmed Abdullahi a gidan gwamnati a makon da ya gabata.
Wata takarda da ya aike wa manema labarai sabon Kwaturolan, Alhaji Ahmed Abdullahi ya ce Gwamnan ya nuna damuwarsa kan cinkosan da gidajen yarin jihar suke fama da shi.
Ya ce Gwamnan ya nuna bukatar a samar da gidan yari mai daukar gadaje 300 a garin Limawa da ke karamar Hukumar Dutse. Ya ce gidan yarin za a gina shi ne irin na zamani mai hade da makaranta da sauran kayan more rayuwa da wurin koyar da fursunoni sanar’o’in hannu.
Ya ce gwamnatin jihar ta yi tunanin haka ne saboda galibin wadanda ake tsare da su a jihar ’yan asalin jihar ta Jigawa ce kuma akwai bukatar gwamnatin ta taimaka wajen inganta rayuwarsu bayan sun kare zaman kaso.
Alhaji Abdullahi ya nuna gamsuwa kan kyakkyawar niyya da gwamnatin na kyautata rayuwa daurarru da jihar, inda ya ce gwamnatin jihar tana matukar taimaka wa gidajen yarin jihar ta hanyar gyara gidan yarin babura da gidan kangararrun yara da ya lalace da gyaran katangar gidan yarin Gumel, tare da gina famfunan tuka-tuka a wasu daga cikin gidajen yarin.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited