Akwai yiwuwar gabatar da batun rikicin Ile-Ife ga Majalisar Dattawa
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Akwai yiwuwar gabatar da batun rikicin Ile-Ife ga Majalisar Dattawa

Akwai yiwuwar gabatar da kuduri a kan batun rikicin Ile-Ife a gaban majalisar dattijwa ta kasa domin tattaunawa da zai sa ayi maganin aukuwar irin haka kwata kwata a nan gaba, inji Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso wanda ya ce, “ba laifi ba ne idan ni (Kwankwaso) ko shi Sanata Jide Omoworare mai wakiltar wannan mazaba ta Ife wani ya gabatar da wannan batu, domin tattaunawa a majalisa. Amma ina tabbatar maka cewa, dukkan abin da ya kamata a yi a yanzu a kan wannan rikici mun gama yin komai. Abin sha’awa a nan shi ne, idan ma mun mika wannan kuka ko bukatarmu ga majalisa, to mun riga mun fara sanar da dukkan sassan gwamnati, musamman hukumar bayar da agajin gaugawa (NEMA) da muka sanar da Darakta Janar, wanda ya yi mana alkawarin aikawa da kayan taimako da za a raba wa mutanen da suka yi asarar dukiyoyinsu.”  Sanata Kwankwaso ya fadi haka ne cikin hira da Aminiya a garin Ile-Ife jim kadan bayan Gwamna Rauf Aregbesola na Jihar Osun ya zagaya da shi sassa daban daban na wuraren da aka yi wa barna a rikicin na makon jiya. Ya ce. “ina matukar farin cikin yadda Gwamna Aregbesola ya tara mana sarakuna da dattawa da masu fada-aji na masarautar Ile-Ife duk da cewa mai girma Ooni na Ife ya yi tafiya zuwa kasar waje amma mun zauna mun tattauna da su da muka fahimci juna tare da yin alkawarin ci gaba da yin aikin hadin kai da goyon baya tare ta yadda za a samo hanyar maganin aukuwar irin haka a nan gaba domin bullar irin haka babbar ill ace ga wannan jihad a kasa baki daya.”
“A saninmu tarihi ya nuna cewa, al’ummar Hausawa sun shafe shekaru fiye da 100 da kafuwa a wannan babbar masarauta ta Ife da ba a taba samun aukuwar irin haka a baya ba. Shi ne ya sa tun farko da na samu labarin faruwar rikicin, sai na fara tuntubar Gwamna Aregbesola da mai alfarma Ooni na Ife da dukkan shugabannin jami’an tsaro na kasa da su hanzarta daukar matakin kwantar da al’amarin wanda aka yi nasarar yin hakan. Inji Kwankwaso wanda ya kara da cewa: “Haka kuma na yi magana da dukkan shugabannin al’ummomin Arewa da kungiyoyinsu da ke zaune a wannan masarauta da muka tabbatar musu da samun kariyar tsaron lafiyarsu da dukiyarsu. Bayan wannan ne na ga cewa, ya dace ni ma in zo da kaina, domin gane wa idanuna komai a inda muka ba ‘yan Arewa shawarar hada kansu da kafa kungiyar amintattu mai karfi da za su bude ajiyar banki (account), wanda za su rinka amfani da shi wajen biyan bukatunsu baki daya. Sun tabbatar mini cewa za su bude wannan ajiya a cikin kwanaki uku, wanda na tabbatar musu cewa, Gidauniyar Kwankwasiya za ta sanya musu tallafin kudi Naira miliyan 10 a cikin wannan ajiyar banki.”

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited