Sanata Kwankwaso ya tallafa wa Hausawan da suka yi asara a rikicin Ile-Ife
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

Sanata Kwankwaso ya tallafa wa Hausawan da suka yi asara a rikicin Ile-Ife

daya daga cikin dattawan Arewacin Najeriya, tsohon Gwamnan Jihar Kano,Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayar da tallafin kudi Naira miliyan 10 ga al’ummar Hausawa mazauna garin Ife-Ife da rikicin kabilanci ya jefa su cikin damuwa a dalilin kashe mutanensu fiye da 50 da kona gidaje da kadarori na miliyoyin Naira da aka yi a makon jiya. Gwamnan Jihar Osun, Ogbeni Rauf Aregbesola shi ne ya fara aikawa da tallafin Naira miliyan biyar da kayan abinci bayan ziyarar gani da ido da ya kai zuwa Ile-Ife kwanaki biyu da aukuwar rikicin.
Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda yake tare da dan majalisar dokoki ta tarayya Hon. Muhammed Garba Gololo ya ambaci bayar da tallafin ne a ranar Talata da ta wuce a lokacin da ya kai ziyarar kwana 1 zuwa  Jihar Osun, domin jajanta wa al’ummar Hausawan da rikicin ya jefa su cikin damuwa. Gwamna Rauf Aregbesola ne ya jagoranci bakin na sa zuwa garin Ile-Ife, inda da suka jajanta wa Hausawan.
Aminiya ta gano cewa, kafin shugabannin su isa garin Ile-Ife a ranar Talata sai da suka yi wata ganawar sirri a ofishin Gwamnan da ke Osogbo a ranar Litinin a inda ake jin sun tattauna ne domin samo hanyar dakile aukuwar irin wannan rikici a nan gaba. Wannan ziyara da dattijan Arewa suka fara yi bayan kwanaki  biyar da barkewar rikicin, alama ce ta kwantar da hankalin jama’ar da aka yi wa barna da samo hanyar yin watsi da bambanci a tsakanin kabilun Najeriya.
A lokacin da Gwamnan yake tarbar Sanata Kwankwaso a ofishinsa ne tawagar Sarakunan Hausawan Jihar Osun su fiye da 20 suka isa ofishin Gwamna Aregbesola, domin nuna farin cikinsu da irin rawar da yake takawa a kan wannan rikici. Shugaban Majalisar Sarakunan Hausawan, Sarkin Hausawan Osogbo, Alhaji Lawal Gwamna shi ne ya jagoranci wannan tawaga da aka dunguma tare da su zuwa garin Ile-Ife.
Sarkin Hausawan Ile-Ife Alhaji Lawal Abubakar Mahmuda Madagali da wasu hakimansa ne suka karbi bakuncin Gwamnan da bakinsa da suka ziyarce su domin ganewa idanunsu irin barnar da aka yi a unguwar Sabo mazaunin Hausawa a rikicin na garin na Ile-Ife.
Cikin jawabin jaje da Gwamnan ya yi wa Hausawan ya fara da nuna matukar bakin cikinsa da aukuwar al’amarin ne, inda ya ba su hakuri tare da tabbatar da cewa kwamitin binciken rikicin da Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya ya kafa yana nan yana aiki, inda ya kama mutane 20 da ake zargi da hannu wajen haddasa rikicin. Gwamnan ya nuna takaicin aukuwar al’amarin, kuma ya jajanta wa Hausawan tare da ba su tabbacin samun kariyar tsaron rayuka da dukiyoyi a yanzu da nan gaba a masarautar Ife da ba a saba ganin irin haka ba. daruruwan mutane Hausawa da Yarbawa, maza da mata da ke zaune a unguwar ta Sabo ne suka saurari bayanai daga bakin Gwamna Aregbesola da Sanata Kwankwaso da jawabin maraba da Sarkin Hausawan ya yi wa bakin. A cewar Sarkin Hausawan : “Aukuwar wannan rikici ya ba mu mamaki kwarai, domin muna zaune lafiya da kabilun Yarbawa da ke harkokin kasuwanci a tare da mu. Wani abin farin ciki shi ne, irin yadda wasu Yarbawa suka boye mutanenmu Hausawa a cikin gidajensu domin tserar da su daga hannun mutanen da suke farautar kashe mu.”
Shi ma Jakadan kasar Nijar a Najeriya, tare da mukarrabansa ya kai irin wannan ziyara zuwa garin Ile-Ife domin yin jaje ga dukkan mutanen da rikicin ya rutsa da su.
Mutanen da Aminiya ta samu zantawa da su musamman mata da suka mallaki shagunan kasuwanci a cikin unguwar ta Sabo, sun nuna matukar bakin cikin aukuwar wannan rikici. Unguwar ta kasance cikin tsauraran matakan tsaro da ci gaba da rufe shaguna da rumfuna , wanda ya haifar da tsayuwar al’amuran yau da gobe, a wannan unguwa da aka saba turereniyar jama’a masu tafiya a kasa da masu abubuwan hawa
Ziyarar Gwamna Aregbesola da bakinsa zuwa Ile-Ife, ita ce ziyara ta biyu da ya kai a cikin kwanaki biyar da faruwar rikicin. Ziyara ta farko ya yi ta ne a ranar Alhamis kwana 1 bayan barkewar rikicin a lokacin yana tare da mataimakiyarsa, Uwargida Titi Laoye-Tomori da wasu mukarrabansa da suka zarce daga unguwar Sabo zuwa fadar Ooni na Ife, Oba Enitan Adewusi. Amma a ziyara ta biyu da Gwamnan yake tare da manyan baki daga Arewacin kasa ba su samu ganin Ooni na Ife ba da aka ce ya yi tafiya zuwa kasar  Birtaniya (a Ingila). Sai dai Gwamna da bakinsa sun samu ganawa da wasu dattawa a karkashin jagorancin magajin gari  Obalufe na Ife, Oba Idowu Adediwura, wanda ya jagoranci daruruwan jama’a maza da mata zuwa babban zauren taro na Ile-Ife da suka saurari jawaban Gwamna da bakinsa a kan wannan al’amari.
Mukaddashin Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Osun DC Aminu Koji, ya yi gum da bakinsa a lokacin da Aminiya ta nemi jin gaskiyar rade radin kama wasu ‘yan sanda da ake zargi da hannu wajen bindige mutane a ranar laraba ta makon jiya da ake cikin rikicin. Shi ma shugaban kwamitin binciken rikicin na Ile-Ife da Sufeto-Janar ya kafa, Kwamishinan ‘yan sanda Hameed Bello, ya ki amsa tambayoyin da aka yi masa a kan rikicin. Sai dai an ga dukkan kwamandojin rundunonin soja da ‘yan sanda da NCSDC da DSS suna jagorantar jami’ansu wajen tabbatar da tsaron lafiyar jama’a da dukiyoyinsu.
Wata majiyar jami’an tsaro da aka sakaya sunanta ta shaida wa Aminiya cewa, “yanzu haka muna neman wasu mutane ruwa a jallo da ake kyautata zaton cewa, su ne suka jagoranci sace buhunan danyen kayan abinci na wake da shinkafa mallakar Hausawa da aka kashe ko aka raunata da suka rinka sayar da mudun wannan hatsi a cikin garin a kan farashi mai rahusan gaske.
Har ila yau, wata majiyar cewa ta yi, kafin jami’an tsaro su kama mata (bayarabiya) da tayi sanadin haddasa wannan rikici sai da tayi nadamar abun da ta aikata wanda mijinta ya yi amfani da matsayinsa na jigo a cikin kungiyar direbobi NURTW ya goya mata baya. Majiyar ta tabbatar da cewa, matar ta taba auren wani B ahaushe da suka haihu tare kafin su rabu.  A ranar Asabar da ta wuce ne Gwamnan Jihar Osun Rauf Aregbesola ya bayar da umarnin suturta gawarwakin mutane 47 dukkansu Hausawa, maza da mata da aka kashe a wajen rikicin na ranar Laraba. An hada duka gawarwakinsu waje daya ne da aka yi masu jana’iza kamar addinin musulunci ya tanadar tare da binne su a cikin babban kabari a garin Osogbo.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited