An karrama Aminiya da lambar yabo a Legas
Monday 26 June 2017     1 Shawwal 1438

Aminiya

A+ A A-

An karrama Aminiya da lambar yabo a Legas

kungiyar Masu Shirya Wasannin Dabe (Wasan Kwaikwayo) na Hausa ta Najeriya ta karrama jaridar Aminiya a binkin da ta shirya na murnar cikar shugaban kungiyar reshen Jihar Legas Alhaji danladi dahiru Zage shekara 53 a duniya.
Shugaban kungiyar ta kasa da ke da hedikwata a gidan dan Hausa a Kano, Alhaji Auwalu Salisu Kolo ya ce sun karrama jaridar Aminiya ce da lambar yabo ta jaridar da ta fi kowace jaridar Hausa a Najeriya a Shekarar 2017, saboda irin gudunmawar da take bayarwa wajen bunkasa al’adun Hausawa da daukaka harshen Hausa, “Jaridar Aminiya ta shahara wajen tsage gaskiya tana tantance labaranta, sannan tana da wakilai a ko’ina wadanda suke zakulo ingantattun labarai da rahotanni masu ilimantarwa da debe kewa, hakan ne ya sanya koyaushe jaridar ke kara samun farin jini, don haka ne muke kokarin kula aminci da Aminiya domin ci gaba da ingata al’adunmu,” inji shi.
Shugaban kungiyar Masu Wasan Dabe reshen Jihar Legas Alhaji danladi dahiru Zage ya nuna godiyarsa ga Allah bisa cikarsa shekara 53 cikin koshin lafiya da wadata. Ya ce sun karrama mutanen da suke ba da gudunmawa wajen gina al’umma kuma suka ga abu ne mafi dacewa su karrama jaridar Aminiya domin gudunmawar da take bayarwa musamman ga mutanen Kurmi wadanda ba su da wata jaridar Hausa da suke samun labarai irin Aminya. “Da Aminiya ne muke sanin halin da duniyarmu ke ciki don haka muka ga ya zama wajibi mu karrama wannan jarida mai albarka,” inji shi.
daruruwan mutane daga sassa daban-daban na kasar nan ne suka halarci bikin taya murnar cika shekara 53 da Alhaji danladi dahiru zage ya yi, bikin da ya gudana a daren Asabar din da ta gabata a Unguwar Agumalu a Legas.

Jaridan Aminiya, Kamfanin Media Trust Limited